Britaniya ta buƙaci Sudan ta bada haɗin kai a game da yankin Dafur | Labarai | DW | 17.10.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Britaniya ta buƙaci Sudan ta bada haɗin kai a game da yankin Dafur

Wata yar Majalisar gudanarwa a gwamnatin Britaniya kuma sakatariyar raya ƙasashe Hilary Benn ta yi kira ga shugaban Sudan Omar al-Bashir ya yarda ya kuma amince da sojin gamiyar ƙasa da ƙasa don aikin kiyaye zaman lafiya a Dafur. Hilary Benn na magana ne a birnin Khartoum inda ta kai ziyara domin ganawa da mahukuntan ƙasar. Benn ta ce har yanzu shugaba al-Bashir yaƙi amincewa da ƙudirin Majalisar ɗinkin duniya domin tura sojoji 20,000 na gamaiyar ƙasa da ƙasa domin kiyaye zaman lafiya a Dafur. A halin da ake ciki soji 7,000 ne na ƙungiyar Afrika ke aikin sintiri a lardin na yammacin Sudan, Benn ta ce sojojin ba sa iya gudanar da cikakken tsaro a yankin baki ɗaya. An ƙiyasta cewa mutane kusan 300,000 ne suka hallaka a Dafur inda kuma wasu mutanen kimanin miliyan biyu da dubu ɗari huɗu suka tagaiyara tun bayan da yaƙi ya ɓarke a yankin a shekarar 2003.