Ana ci gaba da farautar ′yan ta′adda a Turai | Siyasa | DW | 19.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Ana ci gaba da farautar 'yan ta'adda a Turai

'Yan sandan kasar Beljiyam, sun cafke mutane tara, a samame da suka kai dan neman wasu daga cikin mutanen da ake zargi da hannu a hare-haren da aka kai birnin Paris

Bakwai daga cikin wadanda aka kama su na da hannu a harin da aka kai filin wasan kwallon kafan Faransa. Har yanzu dai kasashen Turai na cigaba da mayar da martani dangane da hare-haren na Paris bayan da wani bincike ya nuna cewa wannan kashi farko ne na jerin hare-haren da kungiyar IS ke shirin aiwatarwa a Turai.

Daga cikin wadanda wutan binciken ya rutsa da su har da wani Abdelhamid Abaaoud wanda hukumomi suka ce basu san da shigar shi Faransa ba sai bayan da mutane 129 suka mutu a Paris. kuma kafofin yada labarai sun ce Abaaoud na da hannu a hare-hare da dama wadanda aka kitsa a Beljiyam, tun a watan Janairun wannan shekara, a cewar 'yan sanda.

A yayin da ake cigaba da tsokaci dangane da wannan batu a matakin kasa da kasa, shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel na cigaba da shan suka saboda yawan 'yan gudun hijirar da take dauka wadanda ake zargi 'yan ta'adda na shiga cikinsu ne domin samun damar aikata irin wannan ta'asar. Sai dai duk da haka ta ce ba kasart ba za ta yi kasa a gwiwa wajen tabbatar da 'yancin walwalar al'umma ba

"Wannan take hakkin dan adam din da ake yi ya shafe mu duka, ya shafe dukkanmu da muke raye, wadanda ke da mutunci da walwala da hakuri da juna a zamantakewa, cikin zukatanmu, amma kuma mun san cewa 'yancin walwala ba zai bari a danne shi ba ko da kuwa ta ta'addanci ne ko ta gwamnatocin kama karya"

Abdelhamid Abaaoud Mastermind der Anschlagsserie von Paris

Yan sanda sun kashe jagoran hare-haren Paris, Abdelhamid Abaaoud

Yanzu dai akwai sabbin matakan da Turai ta ke shirin dauka, ministan kula da harkokin wajen Faransa, Laurent Fabius ya ce yaki da ta'addanci na daya daga cikin matsalolin wannan karnin na 21 da muke ciki, kuma Faransa a shirye ta ke ta murkushe shi:

"Kungiyar IS dodo ne amma mambobi dubu 30 suke da shi, yaya za'a yi a ce duk kasashen duniya ba za su iya gamawa da mutane dubu 30 ba, abu ne da kai ba zai dauka ba, Faransa dai a shirye ta ke matuka, mun sani, kuma bai kamata mu yi wa jama'a karya ba, fadan zai dauki lokaci mai tsawo, amma gwamnatin Faransa, a shirye ya ke"

Majalisar dokokin Turai ta gudanar da wata mahawara yau, inda bayan da ta tashi tsaye na minti guda dan tunawa da wadanda harin na birnin Paris ya rutsa da su darektan hukumar 'yan sandan Turai Europol ya ce a yayin da ake juyayin hare-haren da suka faru kamata ya yi a yi dammarar tunkarar abin da ka iya zuwa nan gaba domin barazana ce sosai Turai ke fiskanta:

"Muna tunkarar kungiya ce ta kasa da kasa, mai karfin gaske na wadanda suke da arziki sosai, wadanda kuma suke aiwatar da aiyukansu a kan titunan Turai, saboda haka, kamata ya yi mu san cewa nan gaba hare-haren za su sake afkuwa shi ya sa muke ganin cewa wannan ne barazana mafi karfin da muka taba gani a Turai a tsukin shekaru 10 yanzu"

Ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov ya ce yanayin da 'yan siyasan Turai suka fara duba abin da ya faru ya nuna cewa sun fara nuna dattaku ga batun ta'addancin:

"Kiran da shugaba Hollande ya yi wa shugaba Putin, bayan afkuwar munanan hare-haren Paris, da tayin da yayi na taimakawa yunkurin da ake yi a Siriya, da ma amsar da shugabanmu Putin ya bayar na nuna cewa a shirye ya ke ya hada kai da kawaye sun nuna cewa a yanzu haka 'yan siyas sun fara ajiye kananan abubuwa a gefe domin su tinkari abubuwan da suka fi mahimmanci, kuma sun gane mahimmancin da ya ke da shi a dakatar da IS daga irin hare-haren da take kaiwa yankunan.

Sauti da bidiyo akan labarin