An samu raguwar marasa aikin yi a Jamus | Labarai | DW | 27.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An samu raguwar marasa aikin yi a Jamus

Alkalumman wata-wata da ma´aikatar kwadago ta Jamus ta bayar sun nunar da cewa a cikin watannan na Afrilu yawan marasa aikin yi ya ragu da kimanin mutane dubu 187, abin da ya kawo adadin marasa aikin yi ya zuwa miliyan 4 da dubu 800. Wadannan alkalumman sun nuna raguwar marasa aikin yi dubu 250 idan aka kwatanta da yawansu a cikin watan afrilun bara. To sai dai masana harkar tattalin arziki sun ce an samu wannan ci-gaba ne saboda karin aikin yi da aka saba samu bisa al´ada a farkon kowane lokacin bazara. Shugaban kwamitin zartaswa na kasuwar kwadago ta tarayyar Jamus Frank-Jürgen Weise ya ce kasuwar ba ta farfado da wuri ba saboda matsanancin sanyin hunturu da aka fuskanta a bana, amma duk da haka ya bayyana wannan ci-gaba da cewa mai karfafa guiwa ne.