An nada Ibrahim Gambari a matsayin wakilin MDD na musamman a Iraki | Labarai | DW | 03.03.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An nada Ibrahim Gambari a matsayin wakilin MDD na musamman a Iraki

Babban sakataren MDD Ban Ki Moon ya nada jami´in diplomasiya na Nijeriya Ibrahim Gambari a matsayin wakilin sa na musamman a aikin sake gina kasar Iraqi da MDD ke gudanarwa. Mai magana da yawon sakatare janar din, Michele Montas ta ce aikin malam Gambarin zai kasance karkashin kudurin MDD na taimakawa Iraqi wanda aka amince da shi a shekara ta 2006. A cikin watan yulin bara MDD da gwamnatin Iraqi suka amince da wata yarjejeniyar ba juna hadin kai wajen tafiyar da aikin tallafawa kasar. Wata yarjejeniyar da aka kulla da bankin duniya Iraqi zata samu taimakon sake farfado da tattalin arzikin na tsawon shekaru biyar.