Iraki dai na daga cikin jerin kasashen da ke yammacin nahiyar Asiya. Kasar ta yi iyaka da kasashen da suka hada da Saudiyya da Iran da Siriya.
Galibin al'ummar Iraki Musulmi ne kuma bisa ga kididdigar da aka yi al'ummar kasar baki daya sun kai kimanin mutum miliyan 36. A cikin shekara ta 2003 sojin Amirka suka afka wa kasar bisa zarginta da mallakar makaman kare dangi. Wannan yaki dai shi ya kawo karshen mulkin Saddam Hussein. Amirka ta fice daga kasar a shekarar 2011, sai dai bayan ficewarta rikici ya barke tsakanin mabiya tafarkin Sunnah da 'yan Shi'a.