Iraki ta sa wa′adi na kawar da IS | Labarai | DW | 28.12.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Iraki ta sa wa'adi na kawar da IS

Firaministan Iraki Haider al-Abadi ya ce gwamnatinsu za ta kawar da kungiyar nan ta IS daga kasar a cikin shekara ta 2016 da muke shirin shiga.

Al-Abadi ya bayyana hakan ne a wani jawabi da ya yi ga al'ummar kasar ta gidan talabijin bayan da dakarun kasar suka karbe iko da garin nan na Ramadi daga hannun 'yan kungiyar ta IS.

Firaministan na Iraki ya ce nan gaba kadan kuma dakarunsu za su kutsa kai don karbe iko da garin Mosul wanda shi ne gari mafi girma da ke hannun 'yan IS. Wannan ne ma ya sanya ya ce shekara ta 2016 za ta kasace shekarar samun nasara da ma murkushe 'yan kungiyar Daesh wato IS a Iraki baki daya.