Dakarun Iraqi na samun galaba a kan IS | Labarai | DW | 13.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dakarun Iraqi na samun galaba a kan IS

Dakarun kasar Iraqi na ci gaba da samun galaba a kan 'yan ta'addan IS a garin Tikri.

Musayar wuta a garin Tikrit na Iraqi

Musayar wuta a garin Tikrit na Iraqi

Wani babban jami'in 'yan sandan kasar ta Iraqi da ya nemi a sakaya sunansa ya sanarwa da kamfanin dillancin labaran kasar Faransa AFP cewa jami'an tsaron kasar sun samu nasarar kwace kusan kaso 50 cikin 100 na yankunan da ke garin na Tikrit daga hannu 'yan ta'adda. Sai dai a hannu guda kungiyar IS din ta sha alwashin ci gaba da kai muggan hare-hare a sassan kasar baki daya da kuma kara fadada daularta.