Zirga-zirgar jiragen sama ta dawo tsakanin Rasha da Iraki | Labarai | DW | 17.09.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zirga-zirgar jiragen sama ta dawo tsakanin Rasha da Iraki

Rasha ta sanar da farfadowar zirga-zirgar jiragen sama na kasuwanci tsakaninta da Iraki bayan shekaru 13 da dakatarwa sakamakon matsalar tsaro a Iraki.

Irakisches Luftlinie fliegt wieder

Jirgin Iraqi Airways

Wani jirgi na kamfanin jiragen saman kasar ta Iraki wato Iraq Airways ya tashi a wannan Lahadi da hantsi, inda ya sauka a filin jirgin sama na Vnukovo da ke birnin Mosko a cewar shafin Internet na filin tashi da saukar jiragen saman kasar ta Rasha. Hakan dai na a matsayin wani babban ci gaba ga hukumomin kasar Iraki, abin da ke nunin cewa Rashawa za su iya yin bulaguro kai tsaye zuwa Iraki ba tare da matsala ba. A shekara ta 2004 Rasha ta katse duk wata zirga-zirgar jiragen sama na kasuwanci tsakaninta da Iraki, bayan da harkoki na tsaro suka tabarbare sakamakon kifar da gwamnatin marigayi Saddam Hussein da Amirka da kawayenta suka yi.