Ibrahim Badamasi Babangida tsohon shugaban gwamnati lokacin mulkin sojoji a Najeriya da ya jagoranci kasar daga shekarar 1985 zuwa shekarar 1993.
Babangida ya taka rawa lokacin yakin basasan Najeriya da juye-juyen mulkin da sojoji suka yi a kasar kafin ya jagoranci juyin muliin da ya kawo shi kan madafun iko, inda ya kawar da gwamnatin Janar Muhammadu Buhari.