1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Janar Babangida na so a sake fasalta Najeriya

Uwais Abubakar Idris
June 27, 2017

Tsohon shugaban Najeriya Janar Ibrahim Babangida ya bayyana goyon bayansa kan sakewa Najeriyar fasali, a dai dai lokacin da ake neman shawo kan masu kiran aware.

https://p.dw.com/p/2fUQL
Nigeria Bildergalerie Staatspräsidenten Ibrahim Badamasi Babangida
Janar Ibrahim Badamasi Babangida mai ritaya tsohon shugaban kasar Najeriya na mulkin soja.Hoto: D. Faget/AFP/Getty Images

Fitowa fili da tsohon shugaban Najeriya Janar Ibrahim Badamasi Babangida mai ritaya ya yi na bayyana cewa bai ga laifi na sake wa Najeriyar fasali ba a wannan lokaci wanda ya biyo bayan dadewa da wasu sasassan Najeriya irin na kudu maso gabashin kasar suka yi da ke kama da shagube ga wasu sassan kasar. Koda a lokacin taron kasa da aka yi a 2014 a Najeriya sai da wannan batu ya taso, inda aka watse ba tare da cimma wata matsaya ba.

Nigeria Abuja Nationalrat
Alhaji Shehu Shagari, Janar Ibrahim Babangida mai ritaya, Janar Abdusalami Abubakar mai ritaya, da Chief Ernest Shonenkan sannan da Janar Yakubu Gowon mai ritaya.Hoto: DW/U. Musa

Tuni dai manyan jamiyyun Najeriya suka bayyana goyon bayansu a kan sauye-sauye amma ba batun raba kasa ba kamar yadda wasu matasan sassan kasar suka ambato da ya haifar da tada jijiyar wuya. Suma dai wasu daga jam'iyyar PDP mai adawa sun sanar da nuna goyon bayansu ga wannan batu na kawo gyara amma ba wai raba kasar ba.

Ko da yake Janar Babangida da ya bayyana goyon bayyansa ga masu kokarin a gudanar da sauye-sauye a Najeriya ya ci kashedi ga masu tada fitina da su sani cewa yaki fa ba wasa bane, abinda ya sanya suma daga nasu bangare shugabannin kungiyoyin kwadagon Najeriyar bayyana na su ra'a inda suka watsi da duk wani mai son tayar da fitina.

A yayin da gwamnatin Najeriya ke kokari na dinke duk wata kafa ta fitina ga masu kiraye-kiraye na a raba kasar, har zuwa yanzu babu cikakken bayani a kan shin wa ce hanya za a bi in ma har za a sakewa Najeriyar fasali da mafi yawan masu neman a yi hakan ke hasashen rage wa gwamnatin tsakiya karfi a tsari na shugaba mai cikakken iko.