Bukar Abba Ibrahim tsohon gwamnan Jihar Yobe da ke yankin arewa maso gabashin Najeriya, ya yi mulki na farko daga shekarar 1992 zuwa 1993.
Bukar Abba Ibrahim ya sake zama gwamna daga shekarar 1999 zuwa shekara ta 2007, daga nan kuma ya zama dan majalisar dattawa. Ya kuma rike mukamun kwamishina a tsohuwar Jihar Borno kafin kirkiro jihar ta Yobe.