1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Ibrahim Saminu Turaki

Ibrahim Saminu Turaki dan siyasa kuma tsohon gwamnan Jihar Jigawa da ke yankin arewa maso yammacin Najeriya daga shekarar 1999 zuwa shekara 2007.

Saminu Turaki ya kuma zama dan majalisar dattawa daga shekara ta 2007 zuwa shekara ta 2011, duk da yake an zabe shi gwamnan karkashin jam'iyyar APP wadda ta zama ANPP, amma ya sauya sheka zuwa jam'iyyar PDP a karshen gwamnatinsa, kuma karkashin PDP ya zama dan majalisar dattawa.