An kashe ma′aikatan Julius Berger a Najeriya | Labarai | DW | 31.12.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kashe ma'aikatan Julius Berger a Najeriya

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta tabbatar da kashe wasu Jamusawa guda biyu a karshen makon da ya gabata a wani kauye da ke wajen birnin Abuja.

Kakakin ofishin Ministan harkokin wajen kasar ta Jamus ne dai ya sanar da wannan labari, inda a halin yanzu ofishin jakadancin kasar ta Jamus da ke Najeriya ke ci gaba da binciken kisan gillar, a yayin da rundunar 'yan sandan Najeriyar a ta bakin Kwamishinan 'yan sandan Abujan, ta ce ana ci gaba da binciken wannan batu.

Jamusawan biyu dai sun kasance injiniyoyi na kanfanin kasar ta Jamus na Julius Berger sanannen kanfanin aikin hanya a kasar ta Najeriya. An kashe su a daidai lokacin da suka tafi yawon shakatawa a kan babur, a wasu tsaunuka na kauyen Rinji da ke karkashin gundumar Buwari a kan hanyar Kaduna.

Shaidun gani da ido, sun shaidawa wakilimmu na Abuja cewa, inda aka kashe Jamusawan jeji ne mai hatsarin gaske, duk da cewar Turawa na yawan zuwa tsaunukan a karshen mako domin shakatawa musamman saboda kyawun wurin.