An kama wasu ′yan IS a Jamus | Labarai | DW | 02.06.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An kama wasu 'yan IS a Jamus

Masu shigar da kara na gwamnatin tarayya a Jamus sun sanar da cafke wasu 'yan kasar Siriya guda uku da ake zargin 'yan kungiyar ta'addan IS ne.

Birnin Duesseldorf na Jamus da IS ta shirya kai hari

Birnin Duesseldorf na Jamus da IS ta shirya kai hari

Wadannan mutane dai ana zarginsu da shirya kai wani hari a birnin Duesseldorf na kasar. Masu shigar da karar sun kara da cewa tuni mutum na hudu da ya bayyana shirin kai harin a birnin Paris, ya shiga hannun jami'an tsaro a kasar Faransa. Wata sanarwa da ofishin mai shigar da kara na gwamnatin tarayyar ya fitar, ta ce an cafke mutanen ne a jihohi uku na Jamus a ranar Alhamis biyu ga wannan wata na Yuni da muke ciki, inda ya ce maharan sun tsara cewa mutane biyu za su kai harin kunar bakin wake a tsakiyar birnin na Duesseldorf, kana da ga bisani wani maharin kuma ya bude wuta da bindigogi da kuma abubuwa masu fashewa domin su hallaka mutane da dama.