1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An fara duba lafiyar Alexei Navalny a Jamus

Ahmed Salisu
August 22, 2020

Rahotanni daga birnin Berlin na Jamus na cewar likitoci sun fara duba lafiyar madugun 'yan adawar kasar Rasha a asibitin nan na Charite da ke tsakiyar Berlin.

https://p.dw.com/p/3hLP8
Russland | Alexei Navalny am Flughafen Richtung nach Deutschland
Hoto: Reuters/A. Malgavko

Kamfanin dillancin labaran Jamus na DPA ya ce jirgin da ke dauke da Alexei Navalny ya sauka ne a filin jirgin sama na Tegel kuma kai tsaye aka wuce da shi asibiti inda yanzu haka likitoci ke duba lafiyarsa.

Gabannin isowarsa Jamus dai, Mr. Navalny ya kwanta a wani asibiti da ke birnin Omsk na yankin Siberiya inda aka yi ta kai ruwa rana kafin a bari a fice da shi daga birnin zuwa Berlin don samun kulawar likitoci.

Likitoci a Rasha dai sun ce zargin da ake yi na sanya masa guba a shayi ba shi da tushe balle makama domin kuwa gwaje-gwajen da aka yi masa ba su nuna alamun guba a tattare da shi ba yayin da magoya bayansa suka ce ba haka zance yake ba.