An bude yakin neman zabe a Najeriya | Siyasa | DW | 29.09.2022
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

An bude yakin neman zabe a Najeriya

Jam'iyyun siyasa a Najeriya sun fara aiki gadan-gadan a kokarinsu na ganin sun samu nasara a zaben Najeriya na 2023 bayan da Hukumar Zaben Kasar, INEC, ta amince su fara gangamin yakin neman zabe daga wannan makon.

Nigeria - Verschiebung der Präsidentschaftswahlen

Shugaban Hukumar Zaben Najeriya Mahmood Yakubu

A Najeriya bayar da izinin fara yakin neman zaben da za'a yi a 2023 da hukumar zaben kasar ta yi ya sanya kara kankaman harkokin siyasa a kasar da alummarta suka dade da jiran wannan lokaci. 

Fagen siyasar dai tuni yake amo na yakin neman zaben da ‘yan siyasa suka fara daga ranar Larabar nan, inda suke alkawura na ayyukan da za su yi wa jama'a don fitar musu da kitse a wuta daga hali na rayuwa da suke ciki. A tsari na yakin neman zabe dai kamata ya yi a mayar da hankali a kan batutuwa, amma akasin haka a kan gani a Najeriya. Sai dai babu tabbas ko a wannan karan za ta sauya.

DW.COM

Sauti da bidiyo akan labarin