Shirin soma yakin neman zabe | Siyasa | DW | 26.09.2022
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Shirin soma yakin neman zabe

Yan Najeriya da dama na bayyana fargaba kan yanayin da kasar za ta iya tsintar kai a gabanin soma gangamin yakin neman zaben 2023.

Kasa da tsawon awanni 72 da kaddamar da yakin neman zabe na shugaban kasa a Najeriya faduwar gaba da rashin tabbas na ci gaba da mamaye fagen siyasa ta kasar da ke kallon barazanar hari bisa masu siyasa ta kasar a zaben 2023 da ke tafe.

A jihar Kaduna, an kai ga kame akalla mutane biyu cikin wata tawaga ta dan takara na jam'iyyar APC a zaben gwamna na jihar cikin makon da ya shude a yayin kuma da a jihar Anambara, akalla mutane 10 da ke rakiya ga wani dan majalisar dattawa na jihar aka hallaka, a wani abun da ke kara fitowa fili da irin rikicin da ake shirin fuskanta a fagen siyasa ta kasar.

A tsakiyar wannan mako ne aka tsara kaddamar da yakin neman zabe na shugaban kasar, kuma tuni tsoron ya fara kamari a zuciya da kila bakuna na masu siyasa ta kasar a ko'ina.

Rahotanni na cewa, jiga-jigai na masu takara a mukamai dabam-daban cikin kasar, sun dauki dabarar kare kai da nufin kaucewa tsautsayin da ba shi da rana cikin fagen siyasa ta kasar. Kuma yawan motoci masu sulke da masu siyasar ke saye yana ta karuwa da kila ma wuce ilimin dillallan da ke da jan aiki na biyan bukata ta masu siyasa.

Sabbabi na dabarun tsare kan, na zuwa ne kasa da kwanaki uku da kaddamar da yakin neman zabe na shekarar badi, abun kuma da ke kara fitowa fili da irin barazanar da fagen siyasa ta kasar ke fuskanta yanzu.

Kwanaki 150 da ke tafe na yakin neman zaben na da tasirin gaske ga batu na dimukradiya da kila ma makoma ta kasar da ke rabe a bisa bambancin addini da kabilanci.

Sauti da bidiyo akan labarin