1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Makomar Osinbajo a siyasar Najeriya

Ubale Musa AMA(AH)
July 15, 2022

Da alama rashin nasarar samun tikitin tsayawa jam'iyyar APC takarar shugaban kasa, na neman jefa siyasar Farfesa Yemi Osinbajo a cikin rashin tabbas, bayan zaben fidda gwani na jam'iyyar APC.

https://p.dw.com/p/4EDQo
Nigeria mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo
Nigeria mataimakin shugaban kasa Yemi OsinbajoHoto: Novo Isioro

A baya ana masa kallon taurararuwar jam'iyyar APC, wasu ma na yi masa kirarin Osinbajo magajin Baba Buhari, to sai dai babban taron fidda gwanin jam'iyyar ya mayar da shi a sahun baya da ma shirin karshen rawar da yake takawa a siyasa a matsayin mataimakin shugaban tarrayar Najeriya farfesa Yemi Osinbajo.

Yemi Osinbajo ya rungumi dan kada a cikin jam'iyyarsa ta APC, ya kuma kare jina-jina a siyasar dake neman tilasta masa hakuri. Tsohon mai gidansa Bola Ahmed Tinubu da ya kada shi da farkon fari bai boye bacin ransa da abun da ya kira kokarin cin amanar tsohon yaronsa na fagen siyasa, kana sannu a hankali tauraruwar Osinbajo na rage haske kuma yana komawa kuryar daki cikin jam'iyyar APC.

Karin bayani: Makomar takarar Tinubu da Shettima a Najeriya

Ya kauracewa halartar babban taron tallata dan takarar gwamnan Osun najam'iyyar APC, ya kuma nesanta kansa da wata wasikar da majiyoyin fadar gwamnatin Najeriya ke fadin ya aikewa shugaban kasa, wadda a cikinta yake neman dama ta ritaya daga harkokin jam'iyyar.

Nigeria Farfesa Yemi Osinbajo mataimakin shugaban kasa
Nigeria Farfesa Yemi Osinbajo mataimakin shugaban kasaHoto: Office of Yemi Osinbajo

Abubakar mai Kudi jigo a matasan jam'iyyar APC na kasa, ya bayyana cewa "Yemi Osinbajo na kokarin kaucewa wulakanci ne a tsakanin kabilar sa ta Yarabawa "

Duk da cewar dai ya kai har a mukamin kwamishinan shari'a a jihar Legas, rikicin cikin gida da ke addabar jam'iyyar APC ya tilasta wa mataimakin shugaban kasar fitowa fili ya ayyana kansa a matsayin dan jam'iyyar daga jihar Ogun da nufin kaucewa wani kokarin tozartarwar da ta mamaye zaben fidda gwani a APC.

Karin bayani: Musulmai ne za su yi wa APC takara a Najeriya

An ruwaito mataimakin shugabanNajeriyaa na nuna adawarsa bisa matakin Tinubun na fitar da Musulmi a matsayin a zaben shugaban kasa, lamarin da ke kara ta'azzara rikici a tsakanin mai gida da babban yaronsa.

Ana ganin matakin da ya ragewa mataimakin shugaban shi ne na sake komawa kan mumbarin addini idan sun mika mulki a cikin watan Mayu na 2023, duk da yake na hannun damansa na cewa, ba ya da niyar barin fagen siyasa.