An bude taron kasa da kasa kan yaki da kyamar Yahudanci a Berlin | Labarai | DW | 14.03.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An bude taron kasa da kasa kan yaki da kyamar Yahudanci a Berlin

Taron da majalisar dokokin Jamus ta Bundestag ke karbar bakoncinsa yana samun halarcin wakilai fiye da 100 daga kasashe 40.

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ce kyamar Yahudanci da wariya ba su da wurin zama a kasar ta Jamus. Merkel ta yi wannan furuci ne a wani jawabin da ta gabatar lokacin bude taron majalisun kasa da kasa kan yaki da kyamar Yahudanci wanda majalisar dokokin Jamus ta Bundestag ke karbar bakoncinsa.

Ta ce: "A bayyana yake ga duk mazaunin Jamus da wanda ya jima a nan da ma bakin da ke shigo mana, cewa kyamar Yahudawa da nuna wa wani rukuni na al'umma wariya ba abu ne da za a aminta da shi a Jamus ba. Muna ganin kyamar Yahudanci a bangarori daban-daban na al'umma. Kai hari kan wuraren ibada daidai yake da keta hakkin dan Adam na yin addinin da ya ga dama."

Wakilan majalisun dokoki fiye da 100 daga kasashe kusan 40 ke halartar taron na yini biyu da za a kamma a ranar Talata.