Ambaliyar ruwa a ƙasar Sin ta janyo asarar rayukan mutane 32. | Labarai | DW | 28.07.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ambaliyar ruwa a ƙasar Sin ta janyo asarar rayukan mutane 32.

Ambaliyar ruwar da ke ta addabar yankunan kudanci da gabashin Sin, ya janyo asarar rayukan mutane 32, sa’annan wasu mutane 60 kuma sun ɓace ba a san makomansu ba tukuna. Guguwar iskar nan da aka yi wa suna Kaemi, wadda ta haddasa ambaliyar, yanzu ta wuce yankin kudu maso gabashin Sin ɗin, amma har ila yau ana ta ci gaba da ambaliyar ruwan a jihohi biyar na wannan yankin. Rahotanni dai sun ce kusan mutane miliyan 6 ne annobar ta shafa, kuma tuni an kwashe mutane miliyan ɗaya da ɗigo 3 daga matsugunansu.

A jihar Jiangxi, ɗaya daga cikin jihohin da ambaliyar ta fi ɓarna, mutane 6 ne suka mutu nan take, yayin da zaizayar ƙasa ta binne wani barikin soja jiya da safe. Jami’an ceto a jihar dai sun ce har ila yau kuma, ba a gano sojoji 38 da iyallansu ba tukuna.