Afurka a Jaridun Jamus | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 26.09.2003
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Afurka a Jaridun Jamus

A wannan makon ko da shi ke jaridun na Jamus sun gabatar da rahotanni da dama akan al'amuran nahiyar Afurka, amma muhimmin abin da ya fi daukar hankalin masharhanta shi ne hukuncin da alkalai suka yanke a shari'ar da aka yi wa Amina Lawal bisa zarginta da laifi na lalata. A cikin nata sharhin jaridar Frankfurter Rundschau cewa tayi:
"Duniya gaba dayanta ta kadu a game da hukuncin kisa ta hanyar jifa da duwarwatsu da aka yanke wa Amina Lawal bisa zarginta da laifi na lalata, lamarin da ya sanya shugaba Olusegun Obasanjo ya fuskanci matsin kaimi daga masu fafutukar kare hakkin dan-Adam a sassa dabam-dabam na duniya. Alkalan na kotu shari'a ta Katsina, ko da shi ke sun soke hukuncin sakamakon kurakurai da aka caba wajen ba da shaida a shari'ar da ta gabata, amma fa ita kanta ainifin dokar shari'ar Musuluncin tana nan daran dakau a arewacin Nijeriya. Kuma ko da shi ke bisa ga ra'ayin shugaba Obasanjo dokar shari'ar ta saba da ainifin dokokin kasa, amma ba abin da ya iya tabukawa domin dakatar da aikinta."

To daga Nijeriya zamu durfafi kasar Burkina Faso, wacce ba kasafai ba ne ba jaridun na Jamus ke tabo labarinta a rahotanni da sharhunan da suke gabatarwa. Amma a wannan makon jaridar Neues Deutschland ta leka yankin domin bitar mawuyacin halin da kasar take ciki sakamakon dogaro da tayi akan cinikin auduga wajen samun kudaden shiga na ketare. Jaridar sai ta ce:
"A karkashin wani yunkuri na kakkabe kasarsu daga kurar mulkin mallaka sojoji a karkashin laftana Thomas Sankara suka dauki matakin juyin mulki da canza wa kasar suna daga Upper Volta zuwa Burkina Faso a shekara ta 1983. Amma fa daga baya sai murna ta koma ciki. Domin kuwa a watan oktoba na 1987 mataimakinsa Blaise Compaore ya kifar da mulkinsa sannan ya sanya aka kashe Thomas Sankara da mukarrabansa. Har kuwa ya zuwa halin da ake ciki kasar bata cimma burin da Sankara ya sa a gaba ba na tabbatarwa da al'umarta mutunci da martaba a idanun duniya. Daya daga cikin musabbabin haka kuwa shi ne faduwar farashin auduga da ake ci gaba da samu a kasuwannin duniya, wadda akanta ne kuma kasar Burkina Faso ta dogara wajen samun kudaden shiga. Dukkan biyayya sau da kafa da shugaba Compaore yake yi ga sharuddan asusun IMF da na Bankin Duniya bai tsinana komai ba wajen tayar da komadar tattalin arzikin wannan kasa dake yankin Sahel a yammacin Afurka." Ita kuwa makobciyar kasa ta Cote d'Ivoire ta fuskantar barazanar sake fadawa cikin wata sabuwar rigima sakamakon janyewar da 'yan tawaye suka yi daga gwamnatin rikon kwarya da aka nada a kasar ta yammacin Afurka. A lokacin da take ba da wannan rahoto jaridar Frankfurter Rundschau cewa tayi:
"Bayan da tsofon madugun 'yan tawaye Guillaume Soro ya ba da sanarwar bijire wa gwamnatin rikon kwaryar da aka kafa a tsakiyar wannan mako an kara karfafa matakan tsaro a kewayen kafofin gwamnati dake birnin Abidjan. Dalilin da madugun 'yan tawayen ya bayar a game da shawararsa shi ne rashin sakar wa ministocinsa cikakken ikon zartaswa. Bugu da kari kuma shugaba Laurent Gbagbo yayi fatali da alkawarin da yayi, inda ya nada na gaban goshinsa akan mukaman ministocin tsaro da na cikin gida. Soro ya ce wannan mataki da Gbagbo ya dauka ya sa kafa ne yayi fatali da yarjejeniyar sulhun da aka cimma tsakanin sassan biyu a birnin Paris watan janairun da ya wuce, kuma a sakamakon haka mai yiwuwa 'yan tawayen su sake gabatar da matakansu na yaki."