Afurka a Jaridun Jamus | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 28.11.2003
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Afurka a Jaridun Jamus

A cikin rahotannin da suka gabatar dangane da al'amuran nahiyar Afurka a wannan makon, jaridun na Jamus sun tabo bangarori dabam-dabam abin da ya hada da matsalar cutar nan ta Aids da yake-yake na basasa da kuma dimbim arzikin man fetur da Allah Ya fuwace wa Afurka a gabar tekun Atlantika. A dai wannan makon ne gamayyar mujami'un Afurka suka gabatar da taronsu karo na takwas a Yaunden Kamaru, inda daga cikin batutuwan da aka shigar a ajendan taron har da matsalar nan ta karuwar yawan yaran da akan tilasta musu aikin sojan dole sai kuma yaduwar cutar Aids dake dada yin tsamari a nahiyar Afurka. A lokacin da take ba da wannan rahoto jaridar Die Tageszeitung cewa tayi:
"A dai zamanin baya babu wata rawa ta a zo a gani da mujami'un Afurka suka taka a matakan yaki da yaduwar cutar Aids. Da yawa daga mujami'un, musamman 'yan darikar katolika, su kann bayyana kyamarsu da kiran da akan gabatar na amfani da roba, saboda a ganinsu wannan wani mataki ne dake ba da kwarin guiwa wajen yaduwar lalata tsakanin mutnae. Amma a baya-bayan nan an samu sassaucin wannan manufa ta la'akari da yadda cutar take nema ta zama gagara-badau a nahiyar Afurka."
A halin da ake ciki yanzu madugun 'yan tawayen Hutu da ake zargi da hannu dumu-dumu a kisan kiyashin da ya wanzu a kasar Ruanda a 1994, Paul Rwarakabije ya koma gida bayan sa baki da shugaban Afurka ta Kudu Thabo Mbeki yayi a cewar jaridar Neues Deutschland , wacce ta kara da cewar:
"Shugaba Mbeki na iya buga kirji a game da nasarorin da ya cimma a diplomasiyyance. Domin kuwa bayan sa baki da yayi wajen kusantar da sassan da basa ga maciji da juna a janhuriyar Demokradiyyar Kongo a yanzun ya samu wata sabuwar nasarar a kokarin sasanta rikicin Ruanda. Madugun 'yan tawayen Hutu dake da alhakin kisan kiyashin da ya wakana a kasar a shekarar 1994 kuma hafsan hafsoshin sojan Ruandan James Kabarebe ya tarye shi da hannu biyu-biyu tare da wasu dakarunsa su 100 dake rufa masa baya. Wannan ci gaba da aka samu yana mai yin nuni ne da yadda sannu a hankali ake kokarin warkar da mummunan tabon dake tattare da tarihin kasar ta kuryar tsakiyar Afurka. Wani abin da zai taimaka wajen warkar da tabon kwata-kwata da kuma samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Ruandan shi ne saje wani bangare na dakarun tawayen a sojan kasar da za a ba wa sabon fasali nan gaba."
A dai halin da ake ciki yanzu duka-duka kashi 9% na yawan mai da ake cinikinsa a kasuwannin duniya ne ke fitowa daga nahiyar Afurka, amma ana fatan samun sauyin lamarin na da shekara ta 2010, kamar yadda jaridar Die Tageszeitung ta rawaito a cikin wani dogon sharhin da ta rubuta a game da dimbim arzikin mai dake dirke a tekun atlantika wacce ta hada daga yammaci zuwa kudu maso yammacin nahiyar Afurka. Jaridar dai sai ta kara da cewar:
"A yayinda ake samun raguwar yawan mai da ake haka a sassan duniya dabam-dabam a daya bangaren ana dada samun karuwar bukatar man kuma ana fata nahiyar Afurka zata cike wannan gibi daga nan zuwa shekara ta 2010. Nahiyar ta Afurka tana da dimbim arzikin mai a tekunta, inda daga cikin sabbain adanin mai na garewani miliyan dubu takwas da aka gano a sherkara ta 2001, wannan yanki na Afurka ke da adanin garewani miliyan dubu bakwai. A baya ga haka masu binciken rijiyoyin man sun tashi gadan-gadan wajen binciken wani zirin da ya faro tun daga Nijer ya ratsa kudancin Tchadi zuwa janhuriyar Afurka ta tsakiya da arewa maso gabacin Kongo da kuma yammacin Uganda. Kuma a kurkusa da wannan yanki ne kasar Sudan ta fara cin gajiyar arzikin mai da Allah Ya fuwace mata."
To masu sauraro da wannan muke kammala rahotannin jaridun na Jamus akan al'amuran Afurka sai kuma in ce Zainab gareki.