Afurka a jaridun Jamus | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 05.12.2003
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Afurka a jaridun Jamus

A wannan makon mai karewa jaridun na Jamus sun gabatar da rahotanni da dama a game da nahiyarmu ta Afurka, musamman ma halin da ake ciki a kasar Cote d'Ivoire inda ake fuskantar mummunar adawa akan sojan katsalandan na kasar Faransa. Jaridar Die Tageszeitung ta rawaito rahoto game da haka tana mai cewar:

"Masu adawa manufar zaman lafiya da kuma da wanzuwar sojan Faransa da sauran sojojin kiyaye zaman lafiya na ketare a Cote d'Ivoire sun dage akan lalle sai wadannan sojoji sun janye saboda askarawan kasar su samu gabatar da matakin da suka kira wai na 'yantar da kasarsu. Kasar ta Faransa, wacce ke da sojojin kiyaye zaman lafiya 3800 a Cote d'Ivoire take kuma bakin kokarinta wajen shawo kann rikicin kasar ta yammacin Afurka a cikin ruwan sanyi a yanzu haka ta shiga wani hali na rudu da rashin sanin tabbas. Tuni aka rufe makarantun Faransawan dake Abidjan aka kuma fara kwashe yara domin mayar da su gida Faransa. Gwamnati a birnin Paris dai ta ce ba zata janye sojojin nata ba, tana kuma fatan samun ci gaba lokacin ziyarar da shugaba Gbagbo zai kai Faransa nan da makonni biyu masu zuwa."

Ita ma jaridar Frankfurter Rundschau tayi bitar halin da ake ciki a Cote d'Ivoire inda ta kara da cewar: "Tun bayan da 'yan tawaye suka kakkabe hannuwansu daga gwamnatin hadin kann kasa a misalin watanni uku da suka wuce kasar Cote d'Ivoire ta rabu gida biyu zuwa yankin arewaci dake karkashin ikon 'yan tawaye da kudanci dake karkashin ikon gwamnatin shugaba Laurent Gbagbo. Wani kakakin 'yan tawayen ya ce tilas ne a sa ido a ga yadda zata kaya saboda su kansu sojojin gwamnati suna cikin hali na rudu ne da rashin sanin tabbas". A can janhuriyar demokradiyyar Kongo ana fatan cewar gwamnatin hadin gambiza da aka kafa zata taimaka wajen samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar da yaki yayi kaca-kaca da ita. Amma mujallar Der Spiegel na tababa a game da nasarar wannan gwamnati saboda ta kunshi tsaffin 'yan ta kife ne na kasar. Mujallar sai ta ci gaba da cewar:

"Sabuwar gwamnatin ta Kongo ta kunshi shugaban kasa da mataimakansa su hudu da ministoci 36 da mukaddasan ministoci 25. To sai dai kuma abin takaici wadannan mataimakan shugaban kasa sun hada ne da mutanen da za a kwatanta su tamkar sarakan barayi, wadanda har ya zuwa wajejen tsakiyar wannan shekara suka rika amfani da makamai domin wawason dukiyar da Allah Ya fuwace wa Kongo. Kuma wannan mukami da aka ba su tamkar wata sabuwar dama ce ta cin karensu babu babbaka tare da watandarar da albarkantun kasar. Tun bayan da aka nada maduguwannin 'yan tayae Bemba da Ruberwa mukaddasan shugaban kasa ba a taba samun ko sisin kwabo ba daga cinikin albarkatun kasa da ake yi daga yankunan dake karkashin ikon dakarunsu. Dukkan kudaden suna sulalewa ne ta bayan gida ba wanda ya san makomarsu. Abu daya da za a yi madalla da shi shi ne dagewar da shugaba Joseph Kabila yayi na tabbatar da hadin kann kasar Kongo a karkashin wani yanayi na zaman lafiya da kwanciyar hankali tsakanin illahirin al'umar kasar." A wannan makon aka gabatar da taron kungiyar kasashe renon Ingila da aka fi sani da suna Komonwelt a takaice. Shugaba olusegun Obasanjo mai karbar bakuncin wannan taro ya ki gayyatar shugaba Robert Mugabe na Zimbabwe, wanda a nasa bangaren yayi barazanar ficewa daga tutar wannan kungiya. A lokacin da take ba da rahoto game da haka jaridar Die Tageszeitung cewa tayi: "Cece ku ce da aka rika yi a game da Robert Mugabe dake samun goyan baya daga shuagabannin ATK da Malawi da Namibia, bisa ga dukkan alamu ba ya da tushe, domin kuwa tun da farkon fari shugaban Zimbabwe baya da niyyar halartar taron saboda a karshen wannan makon jam'iyyarsa dake mulki zata gudanar da babban taronta a garin Masvingo kuma tuni aka tanadar da wani farin jirgin sama mai saukar ungulu da zai kai Mugabe dandalin taron".