Afurka A Jaridun Jamus | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 11.06.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Afurka A Jaridun Jamus

A wannan makon jaridun na Jamus sun ba da la'akari da gayyatar da aka yi wa shuagabannin kasashen Afurka domin halartar taron kolin kasashen G8 da aka kammala a jiya alhamis a Sea Island ta kasar Amurka

Tutar taron kolin G8 a Sea Island

Tutar taron kolin G8 a Sea Island

A wannan makon mai karewa jaridu da mujallun Jamus sun gabatar da rahotanni dabam-dabam akan al’amuran nahiyar Afurka. To sai dai kuma muhimman batutuwan da suka fi daukar hankalin masharhanta su ne rawar da Afurka ke takawa a al’amuran tattalin arzikin duniya ta la’akari da gayyatar da aka yi wa wasu shaugabannin kasashen nahiyar domin halartar taron kolin shuagabannin kasashen G8 a Sea Island ta kasar Amurka, sai kuma mawuyacin halin da ake ciki dangane da rikicin kasar Kongo dake neman jefa MDD cikin wani mawuyacin hali na kaka-nika-yi. A lokacin da take gabatar da wannan rahoton jaridar DIE WELT cewa tayi:

"Ko da yake MDD ta tsugunar da sojoji kimanin dubu 11 domin tsaron zaman lafiya a kasar Kongo, amma ga alamu majalisar ta sake shiga wani mawuyacin hali na rashin sanin tabbas. Dubban mutane suka shiga zanga-zanga a fadar mulki ta Kinshasa domin bayyana takaicinsu a game da gazawar sojojin kiyaye zaman lafiyar na MDD, inda aka kashe biyu daga cikin masu zanga-zangar. A makon da ya gabata sojojin na MONUC a takaice sun ba wa askarawan gwamnati damar kutsawa domin kai farmaki kan kabilar Banyamulenge dake da dangantaka da Tutsi a Ruwanda. Amma a yayinda ‘yan tawayen suka mayar da martani suna masu mamayar birnin Bukavu, sai sojojin kiyaye zaman lafiyar na MDD suka zauna sasakai suna masu zura na mujiya akan abin dake faruwa."

Ita kuwa jaridar DIE TAGESZEITUNG tayi sharhi ne tana mai cewar:

"Ta la’akari da barazanar da ake fuskanta a kasar Kongo yanzu haka, mataki na soja ba zai tsinana kome wajen kare makomar shawarwarin zaman lafiyar kasar ta kuryar tsakiyar Afurka, wacce yaki yayi kaca-kaca da ita ba. Wani abin lura a nan shi ne shawarwarin zaman lafiyar ba zasu kai ga tudun dafawa ba sai fa idan an ba da cikakken la’akari ga makomar jin dadin rayuwar illahirin al’umar kasar dake dada shiga hali na kaka-nika-yi. Amma idan manufar ta tuke a tsakanin shuagabannin rukunonin siyasar kasar dake gwagwarmayar kama madafun iko to kuwa kwalliya ba zata mayar da kudin sabulu ba kuma ko ba dade ko ba jima za a wayi gari murna ta sake komawa ciki a game da fatan zaman lafiyar kasar."

A wannan makon shuagabannin kasashen G8 suka gudanar da taronsu a Sea Island ta kasar Amurka, inda aka gayyaci wasu shuagabannin Afurka domin halartar zaman karshe na taron. A lokacin da take ba da rahoto game da haka jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung cewa tayi:

"Shuagabannin kasashen da aka gayyata suna cikin wani rukuni ne na ‘yan gata daga cikin kasashen Afurka dake canjin manufofinsu, wadanda a shekara ta 2001 suka yi hadin kai domin kirkiro manufar nan ta kawancen raya nahiyar Afurka NEPAD a takaice. Manufar gayyatar kuwa shi ne domin kara ba su kwarin guiwa wajen ci gaba da daukar nagartattun matakansu na garambawul a fannoni na siyasa da tattalin arziki."

Ita kuwa jaridar SÜDDEUTSCHE ZEITUNG a cikin nata sharhin cewa tayi:

"Tashi tsaye da Amurka tayi domin tabbatar da zaman lafiyar nahiyar Afurka abu ne dake tattare da dalilai da dama, ba wai kawai yaki da barazanar ta’addanci daga kasashe irinsu Somaliya ba. Babban abin da Amurka take hankoron cimmawa shi ne dimbim arzikin man fetur da Allah Ya fuwace wa nahiyar Afurka tun abin da ya kama daga Nijeriya, Angola, Sudan da sauran kasashen dake makurdadar tekun Guinea. A halin yanzu haka Amurka kan sayo kashi 15% na yawan mai da take bukata ne daga Afurka, kuma tana fata nan da ‘yan shekaru kalilan masu zuwa ta bunkasa yawan abin da take saya daga nahiyar zuwa kashi 25%. To sai dai kuma akasarin wannan arziki yana jibge ne a yankunan da ake fama da rikici a cikinsu kamar Sudan ko kuma gurguncewar al’amuran tsaro kamar Chadi da Nijeriya. Daidaituwar al’amura a wadannan yankuna zata taimaka Amurka ta kayyade yawan dogaro da take yi akan kasashen mashigin tekun Pasha."