Afurka A Jaridun Jamus | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 16.07.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Afurka A Jaridun Jamus

Halin da ake ciki a kasar Kenya na daya daga cikin batutuwan da suka dauki hankalin masharhanta na jaridun Jamus a wannan makon

A wannan makon jaridu da mujallun Jamus sun gabatar da rahotanni da damma akan al’amuran nahiyar Afurka, ko da yake sun fi mayar da hankalinsu ne akan kasar Sudan dangane da ziyarar da ministan harkokin wajen kasar Joschka Fischer ya kai a fadar mulki ta Khartoum. A cikin nata rahoton jaridar Kölner Stadtanzeiger cewa tayi:

"Gwamnatin Sudan ta ki ta cika alkawarin da tayi na kwance damarar mayaka Larabawa a lardin Darfur, a maimakon haka tana wani yunkuri ne na mayar da su wani bangare na sojoji da ‘yan sanda a yankin."

Ita kuwa jaridar Frankfurter Rundschau a cikin abin da ta kwatanta tamkar tafiyar hawainiya cewa tayi:

"Wani abin lura a game da abin dake faruwa a Darfur shi ne ba wanda ya fito fili yayi batu a game da wani mataki na kisan kare-dangi ko tsaftace iri da Larabawa ke dauka akan bakar fata daidai da abin da ya faru a kasar Ruwanda shekaru goma da suka wuce. Dalili kuwa shi ne yin hakan zai wajabta wa MDD tayi katsalandan. A baya ga haka har yau kasashe na daridari a game da kakaba wa gwamnatin Sudan wani tsattsauran mataki na takunkumi kamar haramta sayar mata makamai. A maimakon haka sai aka sa ido ana jiran wai gwamnati a fadar mulki ta Khartoum ta kwance damarar mayakan na Janjaweed."

A nata ra’ayin jaridar Der Tagesspiegel na ganin cewar abu daya da zai taimaka a shawo kan wannan rikici da ya ki ci ya ki cinyewa shi ne hada wani taron da zai kunshi dukkan jinsunan mutane da kabilun da matsalar ta shafa kai tsaye.

Ita ma mujallar Der Spiegel tayi sharhi tana mai cewar:

"Abin takaici shi ne kasancewar manoma ba su da ikon noma gonakinsu saboda dubban daruruwan ‘yan gudun hijirar da suka share fili suka zauna a sassa dabam-dabam na yankin bayan da aka fatattakesu daga yankunansu na asali."

A makon da ya gabata ne aka gabatar da shari’ar wasu shuagabannin kungiyar tawaye ta RUF su uku a Freetown, fadar mulkin kasar Saliyo, domin amsa laifukan ta’asar yakin basasar kasar ta yammacin Afurka. Jaridar Berliner Zeitung ta gabatar da sharhi akan haka tana cewar:

"Kimanin mutane dubu hamsin suka yi asarar rayukansu a yakin basasar kasar Saliyo sannan aka gurgunta wasu dubbanin kuma. A baya ga shuagabannin ‘yan tawaye, wannan shari’a kazalika ta shafi dakarun Kamajo, wadanda ko da yake sun ba wa gwamnati goyan baya amma ana zarginsu da laifuka na muzantawa da azabtar da mutane daidai da ‘yan tawayen."

Wakilan kasashen yammaci a kasar Kenya suna ci gaba da gabatar da kira ga shugaban kasar Kenya Mwai Kibaki game da dagewa akan manufofinsa na yaki da cin hanci. A lokacin da take batu game da haka jaridar Frankfurter Rundschau cewa tayi:

"Ita kanta sabuwar gwamnatin Kenyar ta Mwai Kibaki tana fama da tabargazar cin hanci. An gano wata tabargaza ta karbar toshiyar baki wajen ba da wata kwangilar da ta shafi ayyukan ‘yan sandan ciki da buga nagartattun takardun fasfo. Ta la’akari da haka bai zama abin mamaki ba ganin cewar an fuskanci zanga-zanga mai tsananin a fadar mulki ta Nairobi, inda ‘yan sanda suka yi amfani da barkonon tsofuwa da kulake domin tarwatsa masu jerin gwanon dake Allah Waddai da gwamnatin Kibaki, wacce ta kasa cika alkawururrukan da tayi musu a yake-yakenta na neman zabe."