Afurka A Jaridun Jamus | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 24.09.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Afurka A Jaridun Jamus

A wannan makon masu fafutukar kare hakkin dan-Adam sun soki lamirin Bankin Duniya dangane da matsin lambar da ta saba yi wa gwamnatoci8n kasashe masu tasowa domin mayar da rijiyoyinsu na hakan ma'adinai ga hannun kamfanoni masu zaman kansu, lamarin dake taimakawa wajen gurbata yanayin kasa da tagayyara dubban daruruwan mutane

Ko da yake a wannan makon ma rikicin da ya ki ci ya ki cinyewa a lardin Darfur na kasar Sudan shi ne ya fi daukar hankalin masharhanta na jaridun Jamus, amma zamu fara ne da bitar rahoton da jaridar DIE TAGESZEITUNG ta rubuta dangane da sukan lamirin bankin duniya da masu fafutukar kare hakkin dan-Adam suka yi a wannan mako akan manufofinta a harkar hakan ma’adinai a kasashe masu tasowa. Jaridar ta ce:

"Bankin duniya ya dauki matakai na matsin lamba akan kasashe da dama na nahiyar Afurka domin su danka rijiyoyinsu na hakan ma’adinai a hannun kamfanoni masu zaman kansu da kuma bude kofofinsu ga ‘yan kasuwa na ketare. Amma ga alamu masu ba da wannan shawara ba su yi la’akari da mummunan tasirin da wannan manufa zata yi akan kewayen dan-Adam da kuma mazauna yankunan da lamarin ya shafa ba. A kasar Ghana kadai an fatattaki mutane sama da dubu 30 daga yankunansu na asali domin bude sabbin rijiyoyin hakar zinariya a cikin shekarun 1990. Bugu da kari kuma ba a ba wa manoma isasshiyar diyya akan filayensu na noma da aka kwace. Kazalika dattin masana’antun hakan ma’adinan tuni ya gurbata yanayin kasa da ruwan sha sannan su kuma mazauna yankunan su kan tashi a tutar babu."

Akalla mutane dubu 50 suka yi asarar rayukansu a yayinda duniya ta zura ido tana kallo ba tare da ta tabuka kome ba. Wannan shi ne kanun wani dogon rahoton da mujallar DER SPIEGEL mai fita mako-mako ta rubuta a game da lardin Darfur na kasar Sudan. Mujallar ta ci gaba da cewar:

"Ko da yake abin dake faruwa a Darfur abu ne na bakin ciki da kaico, amma a lokaci guda mummunar tabargaza ce kuma abin kunya ga masu fada a ji a al’amuran wannan duniya tamu. Dukkan kasashen Turai da Amurka sun gaza, inda suka kasa tabuka kome illa maganganu na fatar baki da yin ishara ga ta’asar kisan kiyashin da ta wanzu a kasar Ruwanda a shekarar 1994. A maimakon gabatar da wani sahihin mataki na shawo kan rikicin sai yayata batu suke yi a game da tallafa wa Kungiyar Tarayyar Afurka wajen katsalandan da kuma kiyaye zaman lafiyar lardin Darfur. Ita kanta rundunar kiyaye zaman lafiya ta kasashen Afurka tayi kaurin suna wajen caba kurakurai, misali a kasar Burundi inda ayyukan rundunar ya kai ga zub da jini ko kuma a kasar Liberiya, inda aka wayi gari sojojin kiyaye zaman lafiyar na fafutukar kwasar ganima a maimakon tsaron lafiyar mutanen da suka tagayyara. Wannan gazawar gaba daya ba sabon abu ba ne an fuskance ta dangane da Ruwanda da Bosniya da kuma Kongo da dai sauran yankuna da aka sha fama da kashe-kashe na kare dangi, inda duniya ta saba zura na mujiya ba tare da ta tabuka kome ba."

Al’amura na dada rincabewa a gabacin kasar Kongo sakamakon rikici tsakanin sojoji masu biyayya ga gwamnati da bijirarrun dake karkashin jagorancin kwamanda Laurent Nkumba. A lokacin da take rawaito wannan rahoton jaridar SÜDDEUTSCHE ZEITUNG cewa tayi:

"Kimanin mutane dubu 150 ne suke kan hamnyarsu ta hijira sakamakon tsauraran matakai da sojoji masu biyayya ga gwamnati ke dauka domin murkushe dakarun dake karkashin jagorancin Laurent Nkumba dan usulin kasar Ruwanda, wanda ya ki ya shigar da dakarunsa karkashin laimar gwamnati daidai da yadda yarjejeniyar zaman lafiyar kasar Kongo ta tanada. Kuma ko da yake an cimma daidaituwa tsakanin Ruwanda da Kongo na daukar matakan shawo kan rikicin, amma al’amura ka iya daukar wani sabon salo a game da rikicin na gabacin Kongo da ya ki ci ya ki cinyewa."