Afurka A Jaridun Jamus | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 13.05.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Afurka A Jaridun Jamus

A wannan makon ma halin da ake ciki a kasar Togo shi ne masharhanta na jaridun Jamus suka mayar da hankali kansa

A wannan makon ma halin da ake ciki a kasar Kongo ya kasance daya daga cikin batutuwan da suka fi daukar hankalin masharhanta na jaridun Jamus. Kazalika shirye-shiryen zabe a kasar Habasha da mawuyacin hali na yamutsi a Somaliya da matsalar yunwa dake addabar kasar Eritrea..Amma da farko zamu fara ne da sharhin jaridar Süddeutsche Zeitung ta rubuta ne a game da kasar Togo da sabon shugabanta Faure Gnassingbe, inda take cewar:

“A karo na biyu a cikin dan gajeren lokaci an rantsar da Faure Gnassingbe a matsayin sabon shugaban kasar Togo. To sai dai kuma a wannan karon yana iya ikirarin cewar shi shugaba ne da aka nada sakamakon zabe na demokradiyya. Domin kuwa da farko ya fuskanci matsin lamba daga kafofi na kasa da kasa kamar kungiyar tarayyar Afurka da ta tarayyar Turai lokacin da ya dare kan karagar mulkin kai tsaye bayan rasuwar mahaifinsa Gnassinbe Eyadema watan fabarairun da ya wuce. Amma fa tun da farkon fari ya bayyana a fili cewar Faure ne zai lashe zaben na 24 ga watan afrilu, kuma zai zama abin mamaki da al’ajabi idan ya sha kaye. Wani abin lura a game da wannan batu shi ne duk da cewar yayi murabus sakamakon matsin lambar da ya fuskanta, amma fa Faure Gnassingbe ya ci gaba da zama a fadar mulkin kasar ta Togo yana mai karbar bakuncin maziyarta na ketare da kuma zirga-zirga a jirgin saman da aka tanadar wa shugaban kasa. Ta la’akari da haka da wuya ya kakkabe hannuwansa daga al’amuran mulki.”

A jibi lahadi idan Allah Ya kai mu aka shirya gudanar da zaben majalisar dokokin kasar Habasha. Kuma duk wanda ya duba yadda al’amura ke tafiya a Addis Ababa zai yi imanin cewar kasar na kan hanyarta ta karfafa mulkin demokradiyya, a cewar jaridar Die Tageszeitung, musamman ma ganin cewar a ranar asabar da ta wuce kimanin mutane dubu 100 suka halarci dandalin yakin neman zabe da jam’iyyar gwamnati ta shirya, sannan a kashe gari kuma sama da mutane dubu 200 suka halarci dandalin yakin neman zabe na ‘yan hamayya. Jaridar ta Die Tageszeitung ta ci gaba da cewar:

“Tun da ake ba a taba samun irin wannan cincirindo na dubban daruruwan mutane dake bayyana ra’ayoyinsu a tarihin siyasar kasar Habasha ba. To sai dai kuma duk da wannan ci gaba, wasu kungiyoyi na ‘yan hamayya dake yakar gwamnatin shugaba Meles Zenawi na tattare da imanin cewar babu wani da za a samu. Gwamnati ce zata ci gaba da babakere, a yayinda za a ba wa ‘yan adawa wasu ‘yan kujeru kalilan daga cikin kujeru 547 a majalisar dokokin kasar ta Habasha.”

A halin da muke ciki yanzu haka da wuya zaka tarar da baki ‘yan kasashen ketare dake yawo akan titunan Mogadishu, babban birnin kasar Somaliya. Ita kanta MDD ta mayar da birnin tamkar wani haramtaccen yanki ga ma’aikatanta, a cewar jaridar Frankfurter Rundschau, wadda ta kara da bayani tana mai cewar:

“Daya daga cikin dalilan wannan yamutsi da gurbacewar yanayin rayuwa a Mogadishu shi ne hali na zaman dardar da ake ciki sakamakon yaduwar ‘yan ta kife dake cikin damarar muggan makamai. Kuma ko da yake an sha kokarin kwance damarar dakarun sa kai da suka barbazu a sassa dabam-dabam na Mogadishu, amma har yau ba a cimma biyan bukata ba.”

A wannan makon Jamus ta tsayar da shawarar sake kama dangantakar taimakon raya kasa da kasar Ruwanda. Jaridar Die Tageszeitung ta yi takaitaccen sharhi akan haka tana mai cewar:

“Akwai jami’ai da dama dake sukan lamirin wannan manufa ta taimakon kudi ga kasar Ruwanda saboda ci gaba da mamayar gabacin Kongo da kasar ke yi. Bugu da kari kuma kasar tana amfani da kudaden taimako da take samu daga ketare akan manufofinta na soji, wanda shi ne ainifin abin da ya ba ta ikon shiga a dama da ita a yakin kasar Kongo.”