Afurka A Jaridun Jamus | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 12.08.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Afurka A Jaridun Jamus

Halin da ake ciki a kasar Mauritaniya bayan juyin mulkin da aka gudanar a kasar makon da ya wuce na daya daga cikin batutuwan da jaridun Jamus suka yi sharhi akansu dangane da al'amuran Afurka a wannan makon

Juyin mulkin soja a Mauritaniya

Juyin mulkin soja a Mauritaniya

A wannan makon mai karewa dai jaridun Jamus sun fi mayar da hankali ne akan shirye-shiryen da ake yi na bikin matasa na kasa da kasa a karkashin laimar paparoma Benedikt na 16, bikin da za a gabatar mako mai zuwa a nan Jamus. Amma duk da haka jaridun sun gabatar da rahotanni iya gwargwado akan al’amuran nahiyar Afurka, musamman halin da ake ciki a kasar Mauritaniya bayan juyin mulkin dan kama karya Maawuiya Ould Taya. A lokacin da take ba da rahoto game da haka, jaridar SÜDDEUTSCHE ZEITUNG cewa tayi:

“Kusan babu wata kasa da ta fito tayi suka da kakkausan harshe a game da kifar da mulkin dan kama karyar kasar Mauritaniya Maauiya Ould Taya da aka yi a makon da ya gabata. Kungiyar Tarayyar Afurka ta kebe kasar Mauritaniya daga ayyukanta har ya zuwa wani lokaci nan gaba, a yayinda Amurka tayi Allah Waddai da juyin mulkin. Amma dangane da sauran kasashe, ba wata da ta fito fili ta kalubalanci wannan mataki. Ita kungiyar hadin kan kasashen Larabawa ma cewa tayi wajibi ne a girmama bukatun al’umar Mauritaniya, wanda a fakaice tamkar tana nufin ba da goyan baya ne ga wannan juyin mulki, wanda ya kawo karshen mulkin shekaru 22 na shugaba Ould Taya, wanda shi kansa ya dare kan karagar shugabancin kasar Mauritaniyar sakamakon juyin mulki.”

Ita kuwa mujallar DER SPIEGEL tana hangen wata barazana ce ta billar sabbin tashe-tashen hankula a kasar Sudan bayan mutuwar tsofon madugun ‘yan tawaye John Garang. Mujallar sai ta ci gaba da cewar:

“Ko da yake gwamnati tayi alkawarin bin bahasin hadarin jirgin sama mai saukar ungulu da yayi sanadin mutuwar madugun ‘yan tawaye John Garang, amma har yau mutane na tababa a game da gaskiyar lamarin. Dalili kuwa shi ne, bayan yakin basasa na tsawon sama da shekaru 20 da ya halaka mutane kimanin miliyan biyu, sai ga shi an wayi gari madugun ‘yan tawayen kudancin Sudan ya bakunci lahira makonni uku kacal bayan nadinsa mataimakin shugaban kasa. Wannan sabon ci gaba ka iya zama wata mummunar barazana dangane da makomar yarjejeniyar zaman lafiyar da aka yarfe gumi wajen cimmata tsakanin gwamnati a fadar mulki ta Khartoum da kungiyar SPLA ta kudancin Sudan.”

‘Yan hamayya a kasar Afurka ta Kudu sun tashi haikan domin kalubalantar shirin gwamnati na ba wa makobciyar kasa ta Zimbabwe rancen kudi domin kare ta daga fadawa cikin wata matsala ta fatara. Jaridar FRANKFURTER RUNDSCHAU ta ba da rahoto akan haka inda take cewar:

“Bisa ga ra’ayin ‘yan hamayya a kasar Afurka ta Kudu shawarar da gwamnati ta tsayar game da tallafa wa kasar Zimbabwe da rancen kudi tamkar wani mataki ne na kara tsawwala radadin da al’umar kasar ke fama da shi daga mulkin kama karya na shugaba Robert Mugabe. A makon da ya wuce ne fadar mulki ta Pretoria ta bayyana niyyar ta ta yi na’am da rokon da Zimbabwe ta gabatar na neman rancen kudin da ya kai dalar Amurka miliyan dubu daya, wadanda zata yi amfani da su wajen shigo da muhimman kayayyakin da take bukata, kamar dai man fetur daga ketare da kuma biyan wasu basussukan asusun ba da lamuni na IMF, wadanda wa’adin biyansu ya cika kuma Zimbabwe ke fuskantar barazanar mayar da ita saniyar ware daga asusun na IMF.”

A cikin wata sabuwa kuma gwamnatin shugaba Thabo Mbeki na dada fuskantar matsin lamba a game da sake rabon filin noma bisa koyi da kasar zimbabwe, to sai dai gwamnati ta ki ta ba da kai bori ya hau, inda ta dage akan kudurinta na sayen filayen daga hannun manoma farar fata, wadanda suka tsayar da shawarar sayar da filayen bisa radin kansu, a cewar jaridar NEUES DEUTSCHLAND.