1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afurka A Jaridun Jamus

December 22, 2006

Siyasar Nijeriya na daga cikin abubuwan da jaridun Jamus suka yi sharhi akai a wannan makon

https://p.dw.com/p/BvPS
Shugaban Nijeriya Olusegun Obasanjo
Shugaban Nijeriya Olusegun ObasanjoHoto: dpa

Da farko zamu fara ne da sharhin jaridar NEUES DEUTSCHLAND a kan siyasar Nijeriya, inda take cewar:

„Sannu a hankali tsaffin kurayen Nijeriya na fitowa daga mafakarsu. Domin kuwa bayan da tsofon shugaban gwamnatin sojan Nijeriya Ibrahim Babangida ya bayyana kwadayinsa na sake kama madafun mulki a yanzun magabacinsa shi ma tsofon shugaban mulkin soja Muhammed Buhari ya shiga gwagwarmayar kama madafun mulkin a zaben kasar da za a gudanar a cikin watan mayu mai zuwa, wanda zai kawo karshen shugabancin Olusegun Obasanjo, shi ma dai tsofon dan kama karya na gwamnatin soja, wanda kuma yunkurinsa na yin ta zarce bayan wa’adin mulki karo na biyu ya ci tura.“

A kokarinsa na neman kawo karshen ta’asar dake ci gaba da wakana a lardin Darfur na kasar Sudan, sakatare-janar na MDD mai barin gado Kofi Annan ya nada sabon wakilin Majalisar akan al’amuran Sudan a wani mataki wanda ake gani shi ne na karshe da sakatare-janar din ya dauka. Jaridar FRANKFURTER ALLGEMEINE ZEITUNG tayi bitar lamarin inda take cear:

„A dai halin da ake ciki yanzun ba abin dake nuna cewar za a kawo karshen rikicin lardin Darfur nan ba da dadewa ba, domin kuwa al’amura sai dada yin tsamari suke yi tare da barazanar zama ruwan dare a yankin baki daya. A tsakiyar wannan makon sai da gwamnatin makobciyar kasa ta Chadi tayi zargin cewar dakarun sa kai na Sudan sun kutsa gabacin kasar inda suka kai farmaki kann wasu kauyuka guda biyu tare da kisan akalla mutane arba’in da datse gabobin karin wasu mazauna kauyukan.“

Ita ma jaridar DIE TAGESZEITUNG tayi nazarin lamarin inda take cewar.

„A duk lokacin da mutum ya kara kutsawa gabacin Chadi zai ga sabbin alamomi na mawuyacin halin da aka shiga. Manoma sun kaurace wa gonakinsu a yayinda aka kokkone kauyuka masu tarin yawa. Sojoji da dakarun sa kai a yankin na nuna cewar makobtansu larabawa ne ke da alhakin wannan ta’asa. Wannan rikicin ya kazance ya kuma dauki wani mummunan salo na rashin imani daidai da na lardin Darfur.“

A cikin wani nazarin da tayi jaridar FRANKFURTER RUNDSCHAU ta bayyana mamakinta a game da ake fama da yarfe gumi a kokarin murkushe matsalar yunwa a nahiyar Afurka duk da kyakkyawan ci gaban da ake samu a sauran sassa na duniya. Jaridar ta danganta nazarin nata ne da wani hasashe da Bankin Duniya yayi. Jaridar ta ci gaba da cewar:

„Bisa ga ra’ayin ministar taimakon kasashe masu tasowa ta Jamus Heidemarie Wieczorek-Zeul hasashen da Bankin Duniya yayi abu ne dake ba da kwarin guiwar ci gaba da ba da taimakon raya kasa. Domin kuwa rahoton ya nuna cewar nan da shekara ta 2030 duka-duka yawan mutanen da zasu samu kansu cikin mawuyacin hali na talauci ba zai zarce mutum miliyan 550 ba, wato kimanin kashi 50% na adadin da ake da shi a yanzun. Amma abin ta kaici a rahoton shi ne kasancewar nahiyar Afurka har ya zuwa wannan lokacin zata ci gaba ne da kasancewa ‚yar rakiya, sai fa idan an tashi tsaye an tinkari matsalolin dake hana ruwa gudu ga al’amuran nahiyar kamar dai yake-yake na basasa da sauran rikice-rikice na cikin gida.“