Afurka A Jaridun Jamus | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 11.05.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Afurka A Jaridun Jamus

Bunkasar ciniki tsakanin China da Afurka na daga cikin abubuwan da jaridun Jamus suka yi sharhi kansu

Da farko dai zamu fara ne da duba hadarin jirgin saman nan na kasar Kenya a Kameru, wanda ya dauki hankalin wasu daga cikin jaridun na Jamus. Dalilin haka kuwa shi ne dangane da rawar da kamfanin sufurin jiragen saman na Kenya ke takawa wajen sadarwa tsakanin yammaci da gabacin Afurka da kuma kasancewa tamkar gada mai sadarwa kai tsaye tsakanin nahiyar Afurka da Asiya. Jaridar Die Tageszeitung tayi sharhi akan haka tana mai cewar:

“Kamfanin sufurin jiragen saman kasar Kenya kan yi jigilar fasinja daga yammacin Afurka zuwa kasashe irinsu China da Dubai da Bangkok ko Turkiyya, ba tare da sun bi ta kasashen Turai, inda su kan sha wahala wajen samun izinin ya da zango ba. Kamfanin, bisa sabanin kamfanin sufurin kasar Habasha, ba na gwamnati ba ne, kamfani ne mai zaman kansa, wanda hakan ya taimaka ayyukansa suka zama masu tasiri. Ta la’akari da haka hadarin da aka samu ga jirgin saman a makon da ya gabata ya zama babban koma baya ga kamfanin.”

Asusun tsofon shugaban kasar Amurka Bill Clinton ya cimma wata gagarumar nasara a fafutukar yaki da cutar AIDS, inda wani kamfani na kasar Indiya ya amince da sayar da magungunan cutar akan farashi mai rafusa a kasashe 66 na nahiyar Afurka. Jaridar Frankfurter Rundschau ce ta gabatar da wannan rahoto ta kuma kara da cewar:

“Asusun na Bill Clinton ya cimma yarjejeniya ne tare da kamfanonin Cipla da Matrix na kasar Indiya domin jiyyar masu cutar AIDS akan farashi mai rafusa kuma magungunan wadannan kamfanoni daidai suke da wadanda ake harhadawa a kasashen yammaci masu ci gaban masana’antu. A dai halin yanzu haka mutane kimanin miliyan bakwai ne ke bukatar jiyya akan cutar ta Aids a kasashe masu tasowa.”

A wannan makon kungiyoyin kare hakkin dan-Adam, abin da ya hada har da ta Amnesty, sun zargi kasashen Rasha da China tayi wa kudurin MDD zagon kasa inda suke ci gaba da sayar da makamai ga kasar Sudan duk da takunkumin haramcin da majalisar ta kakaba wa fadar mulki ta Khartoum sakamakon ta’asa da keta haddin dan-Adam a Darfur, a cewar jaridar Die Tageszeitung, wadda ta kara da cewar:

“Hatta a wannan shekarar kasashen Rasha da China sun sa kafa suka yi fatali da kudurin hamarcin sayarwa da kasar Sudan makamai, inda sojojin kasar ke amfani da wadannan makamai a lardin Darfur. To sai dai kuma jaridar ta ce a cikin rahoton da Amnesty din ta bayar a game da wannan zargi bata yi bayani dalla-dalla ba akan samfurin makaman da kasashen biyu suka sayarwa da kasar Sudan.”

Ita kuwa jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung nuna mamakinta tayi dangane da abin da ta kira jahilcin kasashen Turai akan abubuwan dake faruwa a Sudan da Somaliya, wanda ta ce ba shakka shi ne ya sanya kasashen ke dari-dari wajen ba da gudummawa daidai yadda ya kamata ga matakan katsalandan na MDD domin tabbatar da tsaro a wadannan kasashe.

Yunwar danyyun kayayyaki da kasar China ke fama da ita na taimakawa wajen bunkasar kasashen Afurka in ji jaridar kasuwanci ta Financial Times Deutschland a cikin wani don sharhin da ta gabatar a game da dangantakar kasashen Afurka da Chinar a shekarun baya-bayan nan. Jaridar ta ce kasashen Afurka na kudu da hamadar sahara, wadanda aka dade da fid da kauna game da makomarsu suna samun bunkasar da tayi daidai da farko-farkon shekarun 1970 sakamakon cinikinsu da kasar China. A yayinda a shekara ta 1999 ciniki tsakanin sassan biyu ya kama dala miliyan dubu biyu a yanzu ya bunkasa zuwa dala miliyan dubu hamsin kuma ana saran ribanyar lamarin zuwa dala miliyan dubu 100 nan da shekara ta 2010.