Afurka A Jaridun Jamus | Siyasa | DW | 28.04.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Afurka A Jaridun Jamus

Ziyarar Hu ga ƙasashen Afura na daga cikin rahotannin jaridun Jamus akan Afurka

Hu Jintao

Hu Jintao

Halin da ake ciki a ƙasar Chadi na daga cikin muhimman batutuwan da suka shiga kanun rahotannin jaridu da mujallun Jamus dangane da nahiyar Afurka. A cikin nata rahoton jaridar DIE WELT ta lura ne da yadda ƙasar Chadi ke daɗa kutsawa a rikicin Darfur na ƙasar Sudan, inda dakarun ‘yan tawaye dake fafutukar kifar da gwamnatin shugaba Idriss Deby ke da sansaninsu sannan a ɗaya ɓangaren kuma kamfanonin mai na fargaba a game da makomar sabbin rijiyoyin da aka gano a ƙasar. Jaridar ta ƙara da cewar:

“’Yan tawayen ƙasar Chadi dake shirya hare-harensu daga lardin Darfur, waɗanda a ‘yan makonnin da suka wuce suka kutsa har ya zuwa fadar mulki ta N’Djamena ƙokarinsu shi ne su ga sun cimma burinsu kafin zaɓen ƙasar da aka shirya gudanarwa a ranar uku ga watan mayu mai kamawa. Ƙasashen Amurka da Malashiya na bin diddigin wannan rikici tattare da damuwa saboda hannu da kamfanoninsu ke da shi a harkar haƙar mai da aka fara a kudancin Chadi shekaru uku da suka wuce.”

Ita ma mujallar DER SPIEGEL ta leƙa ƙasar ta Chadi inda take cewar:

“Ga alamu shugaba Idriss Deby ya shiga wani mawuyacin hali na ƙaƙa-nika-yi sakamakon adawar da yake fuskanta daga ɓangarori dabam-dabam. Bankin duniya, mai sa ido akan kudaden shiga da Chadi ke samu daga cinikin mai ya tsuke bakin aljifunsa, sannan ita kuma maƙobciyar ƙasa ta Sudan na yi wa ‘yan tawayen Chadi ɗamarar makamai. Ƙasar Faransa, tsofuwar uwagijiyar Chadin ita ce kaɗai, wadda a halin yanzu haka take rufa wa Idriss Deby baya. Shugaban, wanda aka naɗa shi ta hanyar zaɓe, ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan-Adam na zarginsa da yin fatali da manufofi na demoƙraɗiya.”

A wannan makon shugaban ƙasar China Hu Jintao ke ziyarar bita ga ƙasashen Afurka a ƙokarin cike giɓin makamashi da China ke fama da shi sakamakon bunƙasar tattalin arzkin da ƙasar ke samu ba ƙaƙƙautawa, in ji jaridar SÜDDEUTSCHE ZEITUNG, wadda ta ci gaba da bayanin cewar:

“Sannu a hankali ‘yan ƙasar China ke yaɗuwa a dukkan sassa na nahiyar Afurka. Kama daga dudabn-dubatar ‘yan kasuwa da jami’an taimakon raya ƙasa zuwa injiniyoyi da likitoci da ragowarsu. Ma’amallar tattalin arziki tsakanin China da ƙasashen Afurka ta riɓanya har sau goma a cikin ‘yan shekaru goman da suka wuce, inda a yanzu haka ma’amallar cinikin ya kama dalar Amurka miliyan dubu 37 a shekara. Afurka dai tana bukatar kuɗaɗen jari daga ƙetare kuma China ka iya taka muhimmiyar rawa. Abu daya da zai iya zama cikas shi ne zagon ƙasa da Chinar zata yi wa fafutukar da ƙasashen yammaci ke yi na gindaya sharuɗan mulkin demoƙraɗiya da ma’amallarsu da ƙasashen Afurka”

A halin yanzu al’amura sun fara ɗaukar wani tsayayyen fasali dangane da shawarar tura sojojin kiyaye zaman lafiya na ƙasashen Turai zuwa ƙasar Kongo. Jaridar FRANKFURTER RUNDSCHAU ta gabatar da rahoto akan haka tana mai cewar:

“Maƙasundin tura sojojin kiyaye zaman lafiyar na ƙungiyar Tarayyar Turai shi ne domin kandagarkin duk wata husumar da ka taso sakamakon zaɓen shugaban ƙasar da za a gudanar watan yuni mai zuwa, musamman ma daga ɓangaren waɗanda suka yi asarar zabɓen. Ƙungiyar Tarayyar Turai zata tura sojojin ne domin amsa kiran MƊD dake da sojoji kimanin dubu 17 a ƙasar ta Kongo.”