Afurka A Jaridun Jamus | Siyasa | DW | 25.05.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Afurka A Jaridun Jamus

Rawar da Afurka zata taka a taron kolin kasashen G8 ita ce ta fi daukar hankalin jaridun Jamus

A dai halin da ake ciki yanzun rawar da Afurka zata taka a taron kolin gaggan kasashe takwas da suka fi ci gaban masana’antu, wanda za a gudanar a nan Jamus watan yuni mai kamawa, ita ce ta fi daukar hankalin masharhanta na jaridun kasar a wannan mako, kuma ga alamu ita ce zata ci gaba da daukar hankalinsu a makonni masu zuwa. Amma da farko zamu fara ne da wani sharhin da jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta rubuta akan barazanar da kasashen Afurka ke fuskanta na sake shiga wata sabuwar matsala ta dimbim bashi akansu. Jaridar ta ce:

“Kakkabe basussukan dake kansu ke da wuya sai ga shi kasashen Afurka na neman shiga kannun labarai dangane da rancen kudi. Da farko dai kasashe masu matsakaicin ci gaban masana’antu irinsu China sun tashi gada-gadan wajen bai wa kasashen Afurka rancen kudi domin cike gibin da ya samu a garesu sakamakon taka tsantsan da kasashen da suka saba ba da rancen kudin suke yi. A yanzu cinikin dake bunkasa a Afurka shi ne musayar danyyun kayayyaki a madadin rancen kudi.”

Ana zargin sojojin kiyaye zaman lafiya na MDD da laifin fasa-kwabrin zinariya a kasar Kongo. Jaridar Die Tageszeitung ce ta rawaito hakan inda ta ci gaba da cewar:

“Rahotanni sun nuna cewar sojojin kasar Pakistan dake aikin kiyaye zaman lafiya a yankin Ituri na kasar Kongo sun ba da hadin kai ga dakarun gwamnati da kuma ‘yan sa kai domin fitar da zinariya zuwa ketare. Ana zargin sojojin na Pakistan da laifin sayen gwal a Ituri a shekara ta 2005 da kuma sayar da ita ga ‘yan kasuwar dake fitar da ita zuwa ketare ba a bisa ka’ida ba.”

A wannan makon kungiyar neman afuwa ta Amnesty ta gabatar da rahotonta na shekara akan halin da ake ciki dangane da girmama hakkin dan-Adam a sassa daban-daban na duniya. Rahoton nata ya tabo maganar dangantakar Sudan da China domin bayani a game da yadda makomar hakkin dan-Adam zata iya kasancewa a sakamakon huldar tattalin arziki tsakanin kasashen Afurka da na Asiya. A lokacin da take gabatar da rahoto game da haka, jaridar Süddeutsche Zeitung cewa tayi:

“Har yau dai kasar Sudan ita ce tafi kowace kasa a nahiyar Afurka bin manufofi na muzantawa da kuma fama da tashe-tashen hankula. Domin kuwa a baya ga rikicin da ake fama da shi a lardin Darfur akwai kuma barazanar sake billar yakin basasa a kudancin kasar. A cikin rahoton da Amnesty ta bayar an yi nuni da cewar kusan babu wani lardi ko yanki na kasar Sudan da ba a fama da fatattaka da farautar mutane da azabtarwa da kuma hukunce-hukunce na kisa a cikinsa, a yayinda ita kuma China mai kakkarfar alaka da kasashen Afurka take ci gaba da daukar tsauraran matakai akan ‘yan adawa da manufofin gwamnati da kafofi na addinai da yanke hukunce-hukunce na kisa.”

Ta la’akari da wannan ci gaba shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, a wannan makon, ta shirya wani taro tare da gaggan ‘yan kasuwa na Jamus domin ta janyo hankalinsu wajen zuba jari a kasashen Afurka, a daidai lokacin da kasar ke shirye-shiryen karbar bakoncin taron kolin kasashen G8 da suka fi ci gaban masana’antu a duniya. Daga cikin muhimman bangarorin da za a iya zuba jari a cikinsu har da hanyoyin sadarwa, wadanda asalan ma dai sune madogarar ci gaban tattalin arzikin kasa, in ji jaridar Die Tageszeitung, wadda ta rawaito wannan rahoto.