1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afrika A Jaridun Jamus

Mohammad Nasiru AwalJanuary 30, 2004
https://p.dw.com/p/BvqC
To a wannan makon mai karewa ma dai jaridun na Jamus sun rubuta sharhunan da dama game da nahiyarmu ta Afirka musamman dangane da rikice-rikice da suka ki ci suka ki cinyewa a wannan nahiya. A cikin wani sharhi da ta rubuta jaridar TAGESZEITUNG ta rawaito wakilinta a yankin dake kewayen Nyabibondo mai tazarar kilomita 20 gabas da Bujumbura babban birnin kasar Burundi na cewa dubun dubatan fararen hula a wannan kasa dake fama da yakin basasa a Gabashin Afirka, sun tsere daga wani sabon fada da ya barke tsakanin wasu kungiyoyin kabilar Hutu biyu da ba sa ga maciji da juna. Wakilin ya labarto wani dan gudun hijira na cewa wasu tsofaffin ´yan tawayen kungiyar baradan kare demukiradiyya wato FDD sun kaiwa ´ya´yan kungiyar National Liberation Front hari. Wani jami´in dakarun gwamnati ya tabbatar da hakan, inda ya kara da cewa sojojin gwamnati sun kaiwa ´ya´yan kungiyar FDD dauki. Bayan ta sanya hannu akan yarjejeniyar samar da zaman lafiya a ran 16 ga watan nuwamban bara, kungiyar ta FDD ta samu wakilci a cikin gwamnatin hadin guiwa wannan kasa dake karkashin ´yan kabilar Tutsi.

Ita kuwa jaridar FAZ labari ta bayar game da fadan da ake ci-gaba da gwabzawa a yammacin kasar Sudan, wanda ya tilasta mutane sama da dubu 100 tserewa daga wannan yanki zuwa kasar Chadi. Jaridar ta ce a daidai lokacin da ake samun ci-gaba a tattaunawar samar da zaman lafiya da ake yi tsakanin gwamnatin birnin Khartoum da ´yan tawayen kungiyar SPLA, sai ga shi ana gwabza fada a yammacin kasar duk da sanarwar dakatar da yaki na tsawon makonni 3 da aka bayar. Wadanda suka tsere daga yankin na Dafur sun ce jiragen saman yakin gwamnati na yawaita yin lugudar wutar akan wannan yanki. Ba kamar rikicin kudancin kasar tsakanin gwamnati da ´yan tawaye ba, wannan fadan da ake yi a yankin na kan iyakar Sudan din da Chadi, ba shi da nasaba da addini, domin kusan dukkan al´umar Dafur din mabiya addinin musulunci ne. Al´umar wannan yanki dai na bukatar a inganta halin rayuwarsu ne, kasancewar yankin nasu ya shafe shekaru da dama ba tare da samun kulawar gwamnatin birnin Khartoum ba.

Ita ma jaridar Frankfurter Rundschau ta yi tsokaci game da mawuyacin hali da ´yan gudun hijirar yankin na Dafur dake yammacin Sudan suke ciki. Jaridar ta ce a halin da ake ciki ´yan gudun hijirar da ke wani sansanin kan iyakar da Chadi na bukatar taimakon kayan abinci da magunguna. Jaridar ta ce abin takaici ne ganin cewa har yanzu babu wata alamar tsagaita bude wuta tsakanin kungiyoyin ´yan tawaye da dakarun gwamnati dake kece raini a wannan yanki. Hasali ma shawarwarin samar da zaman lafiya da ake yi tsakanin gwamnati da ´yan tawayen kungiyar SPLA da nufin kawo karshen yakin basasan da aka shafe shekaru 20 ana yi a kudancin kasar ya gamu da cikas, domin yanzu haka an dakatar da wadannan shawarwarin bisa dalilan cewa mataimakin shugaban kasa, Ali Osman Taha dake wakiltar gwamnati, ya tafi kasa mai tsarki don yin aikin hajji.

A wani sharhi da ta rubuta har wayau jaridar FR ta rawaito majiyoyi na diplomasiya a birnin Nairobin din Kenya na cewa mahalarta taron samar da zaman lafiya a kasar Somaliya sun amince da wani daftarin kundin tsarin mulkin kasa na wucin gadi. To amma ba´a samu daidaito game da wasu batutuwa da dama ba. Wannan daftarin tsarin mulkin ya tanadi kafa majalisar dokoki mai wakilai 275 daga dukkan kabilun wannan kasa. Ko da yake masu nazarin al´amuran yau da kullum na ganin za´a dauki lokaci mai tsawo kafin a samu wanzuwar zaman lafiya a wannan kasa, amma amincewa da wannan daftarin wani mataki ne akan turbar da ta dace. Yanzu kuma bari mu kammala da wani sharhi da jaridar TAZ ta rubuta mai taken Afirka ta kafa wata sabuwar kotu. To sai dai tun tafiya ba ta yi nisa ba, wannan kotu da aka kafa da nufin bitar kararrakin take hakkin dan Adam, tana fuskantar barazana ta rugujewa, saboda matsalolin na rashin isasshen kudin tafiyar da aikinta. Tun dai a ran lahadi da ta wuce wannan kotu ta kafu a hukumance, kuma duk da cewa kasashen kungiyar tarayyar Afirka sun amince da kafuwarta, amma har yanzu ba´a san kasar da wannan kotu zata rika yin zaman sauraran shari´a ba. To Allah Ya kyauta.