AFCON 2019: Kasashe 24 sun samu tikitin shiga gasar | Zamantakewa | DW | 25.03.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

AFCON 2019: Kasashe 24 sun samu tikitin shiga gasar

Kasashe 24 sun samu tikitin shiga gasar cin kofin kwallon Afirka ta 2019 da za a yi a Masar. A nan Turai kuma Jamus ta lalasa kasar Holland a wasan neman shiga gasar cin kofin kwallon kafa ta Turai ta 2020.

A cikin shirin namu na yanzu za ku ji cewa a halin yanzu kasashe 24 da suka samu tikitin shiga gasar cin kofin kwallon Afirka ta 2019. A nan Turai kuma Jamus ta lalasa kasar Holland a wasan neman shiga gasar cin kofin kwallon kafa ta Turai ta 2020.

Bari mu bude shirin namu da gasar cin kofin kwallon kafa ta Afirka ta 2019 da za ta gudana a kasar Masar daga ranar 21 ga watan Yuni zuwa 19 ga watan Yuli inda a karshen mako aka yi karawar karshe da ta ba da damar fito da kasashe 24 da suka samu tikitin shiga gasar. Kasashen guda 24 da suka samu tikitin shiga gasar ta 2019 sune Senegal da Madagaska a rukunin A, Maroko da Kamaru a rukunin B, a rukunin C Mali da Burundi , Aljeriya da Benin a rukunin D, Najeriya da Afirka ta Kudu daga rukunin E, Ghana da Kenya a rukunin F,Zimbabuwe da Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango daga rukunin G, Guine da Cote d'Ivoire a rukunin H, daga rukunin I Angola da Moritaniya, Tunusiya da Masar mai masaukin baki daga rukunin J, Guine Bissau da Namibiya a rukunin K, Uganda da Tanzaniya a rukunin L. Sai dai kuma Daya daga cikin wasannin da suka fi daukar hankali a fafatawa 24 da aka yi a krashen mako, ita ce wacce aka yi tsakanin gagararrun zakunan kasar Kamaru wacce aka karbi shirya gasar daga hannunta da kuma kasar Komoro a ranar Asabar a filin wasa na Ahmadou Ahidjo. Daga karshe dai Kamaru ta samu tikitin nata bayan da ta lalasa Komoro da ci uku da babu. 

Karawa tsakanin Jamus da Holland a birnin Amsterdam. Jamus 3, Holland 2

Karawa tsakanin Jamus da Holland a birnin Amsterdam. Jamus 3, Holland 2

Har yanzu dai muna kan batun kwalon kafan amma a nan Turai inda aka soma wasannin tankade da rairaye na neman cancantar shiga gasar cin kofin kwalon kafa ta Turai ta shekara ta 2020 wacce a karon farko a tarihi za ta gudana a tsakanin birane 12 na Turai , biranen da suka hada da London a Ingila. Bakou a Azerbeijan, Cophenhegen a Danemark, Munich na Jamus, Budapest a Hungari, birnin Roma na Italiya, Amsterdam a kasar Hollande, Dublin na Ayland, Bucarest na Roumaniya, Seint Petersburg na kasar Rasha, Glasgow a Scotland, da birnin Bilbao na Spain. kasashe 55 ne a cikin rukunnai 10 za su fafata a karawa 262 inda daga karshe za a fito da kasashe 24 da za su halarci gasar wacce za ta wakana daga ranar 12 ga watan Yuni zuwa 12 ga watan Yuli. Wasannin da suka fi daukar hankali Daga cikin wasannin tankade da rairayen wannan gasa da suka wakana a karshen mako sune kashin da Kuroshiya a Hangari da ci biyu da daya da kuma nasarar da Jamus ta yi a kan kasar Hollande da ci biyu da uku. 'Yan wasan gaba Leroy Sane da Serge Gnabry suka ci kwallayen farko tun a mintuna 45 na farko a yayin da dan wasan baya na gefe Nicko Schulz ya ci wa Jamus a minti na karshe na wannan wasa.

Sauti da bidiyo akan labarin