Kasar Netherlands ko Holland wata karamar kasa ce a yammacin nahiyar Turai. Babban birninta shi ne Amsterdam wanda ruwa yake kewaye da shi.
Kasar na daga cikin wadanda suka jagoranci kafa kungiyoyin da suka hada da NATO da EU. A ita wannan kasa ce ake da kotun ICC da ke birnin The Hague ko Den Haag a harshen al'ummar kasar. Holland ce ke da tashar jiragen ruwa mafi girma a Turai wadda ke birnin Rotterdam.