1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekarar mai tattare da kalubalai ga al'ummar Najeriya

Uwais Abubakar Idris AMA
January 2, 2021

Ana bukukuwan shiga sabuwar shekara ta 2021 a daidai lokacin da jama'a a Najeriya ke tunawa da shekarar 2020, da ta kasance mai tattare da kalubalai ta fannoni dabam-daban ga al'umma.

https://p.dw.com/p/3nPZf
Nigeria Feier 60 Jahre Unabhängigkeit
Shugaba Muhammadu Buhari a yayin bikin cikar kasar shekaru 60 na 'yancin kaiHoto: Kola Sulaimon/AFP

Abubuwan da suka faru a 2020 a Najeriyar sun fi karkata a kan batun rashin tsaro wanda aka bude shekarar ta 2020 mai karewa da shi, domin baya ga hari na Kungiyar Boko Haram da ta soma tun a farkon watan Janairun, munanan hare-hare ciki har da wanda ta kai kan manoman shinkafa tare da kashe sama da 70 a Zabarmari tajihar Borno ya dauki hankali sosai a Najeriyar.

Ta’azarar da matsalar masu satar shannu da garkuwa da jama’a ta yia Najeriya ta durkusar da harkokin yau da kullum musamman a yankin Arewa maso yammacin kasar, satar daliban sakandaren Kankara da a watan Disambar 2020 ya ja hankalin duniya ba ma al'ummar Najeriyar kadaii ba. 

Karin Bayani: Yawaitar kananan makamai a Najeriya

Matsalar tsaro ta gamu da annobar Covid-19

Karikatur Die 2. Corona-Welle in Nigeria
Hoton barkwanci na annobar coronavirus

Annboar coronavirus ta bullu a Najeriya a daidai lokacin da jama'a ke cikin matsalar tsaro, inda tun a watan Febrairu kasar ta samu mutum na farko da ya dira a cikinta dauke da cutar sarkewar numfashi ta Covid-19, cutar da ta yi ta karuwar har ta kai ga tilasta wa gwamnatin Najeriyar rufe duk wata zirga zirga a kasar, lamarin da ya dauki kusan daukacin shekerar 2020, tare da yin mumunan illa ga fannin tattalin arzikin Najeriya.  

To sai dai duk da fadi tashi da hali na rayuwar da ‘yan Najeriya suka samu kansu a ciki, musamman karuwa na kuncin rayuwa ga Barrsiter Mainasara Umar mai sharhi a fanin al’amurran yau da kullum na kalon shekara ta 2020 mai cike da muhimman abubuwa ga Najeriya da dimukurdiyyar kasar inda ya bayyana ci gaban da aka samu ta fannoni dabam-daban na dimukuradiyyar Najeriya.

Karin Bayani: Najeriya kasa mafi karfin tattalin arziki a Afirka

Lalurar fyade ta addabi Najeriya a 2020
An fuskanci yawaita fyade a Najeriya, ba ga babban mutun ba balantana karami, an ci zarafin yara kanana wadanda shekarunsu ba su wuce biyu zuwa 10 ba, an yi wa wasu fyade a Najeriya har ya zama ajalinsu, to amma sai dai an bullo da sabbin hanyoyin na dakile matsalar da ta addabi musamman arewacin Najeriya. Kungiyoyin mata da gwamnati sun tashi haikan kan wannan matsalar, to amma har yanzu da akwai sauran rina a kaba. 

Zanga-zangar ENDSARS ta girgiza Najeriya 
An dai ga mumunan zanga-zanga mafi muni da ta matasa suka yi a Najeriyar wacce suka tilastawa gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari rusa  sashin ‘yan sanda na SARS tare da maye gurbinta, ko za’a ce shekara ce da ba’a fatan Allah maimaita ierinta ga 'yan Najeriya? A ya yinda ‘yan Najeriya ke ban kwana da shekara ta 2020, da dama na cike da fata da burin a samun alkhairai mafi inganci a sabuwar shekarar 2021 da ta kama.

Nigeria Lagos | Protest EndSARS
Zanga-zangar EndSARS a Lagos NajeriyaHoto: Adekunle Ajayi/NurPhoto/picture-alliance

Karin Bayani: Jaridun Jamus sun yi magana kan #EndSARS