Dokar ta-baci kan fyade a Najeriya | Labarai | DW | 12.06.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dokar ta-baci kan fyade a Najeriya

Gwamnoni a Najeriya, sun kaddamar dokar ta-baci a kan matsalar fyade ga mata da ke ci gaba da karuwar a kasar a wannan lokaci da yankuna da dama ke dokar kulle.

A kusan karshen yinin ranar Alhamis ne dai gwamnonin Najeriya 36 suka fitar da matsaya a kan wadanda ke aikata wannan kazamar dabi'a, bayan zanga-zangar da ta karade kasar da ke nuna gajiya da lamarin.

A jawabin da ya yi wa 'yan kasar albarkacin cikar kasar shekaru 21 da kama tafarkin dimukuradiyya, Shugaba Muhammadu Buhari ya ce ya kadu matuka da yadda fyade ke karuwa a Najeriyar, musamman na kananan yara mata.

Shi ma ministan shari'ar kasar, Abubakar Malami, ya ce nan ba da jimawa ba za a kaddamar da kwamiti a dukkanin manyan ma'aikatu na gwamnatin tarayya wadanda za su tsara hanyoyin sauya hukunci kan cin zarfin na mata, hukuncin kuma da zai dace da ko'ina a duniya.