1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mayakan Boko Haram sun hallaka manoma a Borno

Abdourahamane Hassane
December 3, 2020

Mayakan Boko Haram sun hallaka manoma 76 a yanki arewa maso gabashin Najeiya a Jihar Borno inda suka kai hare-hare a cikin gonaki da dama hakan ya janyo cikas a kan sha'anin noma.

https://p.dw.com/p/3mB5C
Nigeria Reis-Produktion
Hoto: Imago Images/photothek/T. Imo

Wannan al'amari na kisan manoman a Najeriya ya janyo muhawara game da gazawar sojojin Najeriya wajen kare lafiyar al'umma da dukiyoyinsu, kana ya kawo cikas a kan sha'anin noma wanda ya ja baya.Har yanzu al’ummar yankin Koshebe da Zabarmari na cikin rudani saboda komai na harkokin noma da su ke yi ya tsaya sakamakon barazana da da mayakan Boko haram su ka musu na cewa duk wanda ya fita gona za su hallaka shi.