1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwa

Najeriya za ta tsaurara dokokin fyade

June 11, 2020

Wani matakin da ke zaman taunin tsakuwa da nufin aiken sako gwamnatin Najeriya tana shirin tabbatar da daurin rai da rai  ga masu laifin fyade domin dakile matsalar da ke ci gaba da yaduwa a cikin kasar.

https://p.dw.com/p/3ddgx
Nigeria | Frauen protestieren gegen Gewalt und sexuelle Belästigung durch Polizisten
Hoto: DW/U. Abubakar

Kama daga jihar Kano da a wannan mako aka kama wani mutum guda daya da yi wa mata 40 fyade cikin gari daya ya zuwa Anambra inda aka samu kimanin iyaye 80 sun yi wa 'ya'yansu fyade a cikin kullen Covid-19.

Can a jihar Edo ma dai an kai ga halaka wata budurwa bayan yi mata fyade a harabar wata majami'a cikin jihar a makon da ya shude. Tuni aka samu ta'azzarar al'adar fyade a ko'ina cikin Najeriya ya zuwa yanzu.

To sai dai kuma  gwamnatin kasar tace daga yanzu kuma duk wanda aka samu da laifin aikata fyade a cikin tarrayar najeriya to zai fuskanci tsanani na hukunci kama daga dauri na rai da rai ya zuwa hukunci na kisa kamar yadda dokar hana fyade ta kasar ta tabbatar.

Nigeria Kampf um Frauenrechte
Hoto: Getty Images/AFP/K. Sulaimon

Pauline Tallen ministar mata ta Najeriya ta ce yawan karuwa kan fyade a kasar ya nunka har gida uku sakamakon zaman gida na Covid-19. Kuma a fadar ministar matan lokacin jan shari'a ko kuma yanke hukuncin tara ya kare ga masu al'dar fyaden kama a bangare na gwamnatin tarayya ko kuma su kansu jihohi na kasar.

Abun jira a gani dai na zaman yadda matakan 'yan mulkin ka iya shawo kan annobar da ke neman komawa ruwan dare gama duniya a kasar bisa hujjojji iri-iri.