1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fafaroma ya koka da kisan manoma a Najeriya

December 2, 2020

Jagoran darikar Katholika na duniya, Fafaroma Francis, ya yi Allah wadai da kisan wasu gwamman manoma a kauyen Zambarmari da ke jihar Bornon Najeriya a karshen makon jiya.

https://p.dw.com/p/3m7RM
Vatikan Papst Franziskus
Hoto: Stefano Spaziani/dpa/picture-alliance

Fafaroma Francis wanda ya kwatanta kisan manoman da ake zargin mayakan Boko Haram da aikatawa da kisan kiyashi irin na ta'addanci, ya kuma wannan wani abu ne da yake matsayin babban laifi.

A jawabin da ya yi a fadarsa ta Vatican, ya yi alkawarin yi wa Najeriya addu'o'i, kasar da ke fama da rikice-rikice da ke haddasa matukar asarar rayuka.

Ya zuwa yanzu dai babu wata kungiyar da ta dauki alhakin harin wanda aka dora kan mayakan tarzomar Boko Haram.