1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus za ta taimaka wa yankin Sahel

April 15, 2022

Jamus ta nemi a hada karfi da karfe don shawo kan matsalar sauyin yanayi wacce ta kasance tushen sauran matsalolin da yankin Sahel ke fuskanta in ji Baerbock a ziyarar aiki a Nijar.

https://p.dw.com/p/49y1k
Außenministerin Baerbock besucht Mali
Hoto: Kay Nietfeld/dpa/picture alliance

Ministar harkokin wajen Jamus Annalena Baerbock ta jagoranci wata lakca a jami’ar birnin Yamai na jamhuriyyar Nijar, kan batun alakar da ke da akwai tsakanin matsalar sauyin yanayi, da ta karancin abinci da kuma ta tsaro a yankin Sahel da kuma gudunmawar da Jamus za ta iya kawo wa kasashen na Sahel wajen shawo kan wadannan matsaloli.

Niger | Flüchtlingslager bei Ouallam | Besuch Annalena Baerbock
Baerbock ta gana da 'yan gudun hijirar OuallamHoto: Richard Walker/DW

Ministar harkokin wajen kasar ta Jamus Baerbock wacce ta soma wata ziyarar aiki ta kwanaki a kasar ta Nijar, ta kwashe kusan awa daya tana gabatar da bayani a gaban daruruwan dalibai da malaman jami’ar birnin Yamai kan matsalar sauyin yanayi da kuma alakar da ke da akwai tsakanin wannan matsala da ta karancin abinci da ma ta tsaro a yankin na Sahel.

Kazalika ta kuma yi bayani kan irin rawar da Jamus ke takawa a cikin wannan kokowa a Sahel inda amma ta bayyana bukatar hada karfi da karfi domin tunkarar matsalar sauyin yanayi wacce ta ce ita tushen sauran matsalolin. 

Außenministerin Annalena Baerbock besucht Mali
Baerbock a ganawa da Assimi Goita na MaliHoto: Florian Gaertner/Auswärtiges Amt/Photothek/dpa/picture alliance

Ta ce, ''Mun gani kuma mun ji zahirin wannan matsala ta sauyin yanayi a wannan yanki, mun fahimci kuma alhakin da ke kanmu da wajen da ya haifar da wannan matsala, shi ya sa muka fara karfafa hulda da kasashen yankin a fannin yaki da sauyin yanayi da kuma samar da makamashi, amma maganin matsalar shi ne, ba yakar matsalar ba akan takarda, mu dage ya kasance a zahiri kuma yana daga cikin muhimman matakai na magance matsalar sauyin yanayi''

A wannan Alhamis ministar harkokin wajen kasar ta Jamus za ta kai ziyara a Ouallam cikin Jihar Tillabery  inda za ta ziyarci sansanin ‘yan gudun hijira na Mali dana Nijar kafin da yamma ta halarci taron manema labarai hadin gwiwa da takwaranta na Nijar ta kuma karkare da ganawa da Shugaban Mohamed Bazoum a fadarsa.