1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: An dawo da aiki da Babura a jihar Tillabery

Gazali Abdou Tasawa
September 1, 2021

A Jamhuriyar Nijar a wannan Larabar ce aka koma aiki da babura a jihar Tillabery, bayan share shekaru hudu a karkashin dokar hana amfani da babura a jihar baki daya saboda dalillai na tsaro.

https://p.dw.com/p/3zn8H
Niger Niamey Proteste AREVA Uran
Hoto: DWM. Kanta

Mahukuntan jihar ta Tillabery sun sanya sharudda na sake komawa amfani da baburan amma duk da haka al’ummar yankin na cike da farin ciki da wannan mataki kamar yadda Assaguide Mounkaila, mataimakin magajin garin birnin na Tillabery ya baiyana.

 "Ya ce kafin mutum ya koma amfani da babur sai ya kawo shi ma’aikatar magajin gari, tare da duk takardun babur din. A nan za a yi masa rijista a bashi wata takarda wacce ke kunshe da bayanai na lambar babur din da launinsa. Sannan izinin hawan babur din na farawa daga karfe shida na safe zuwa karfe bakwai na yamma" 

Sai dai duk da wadannan sharudda jama’a na cike da farin cikin komawa aiki da baburan kuma da dama daga cikinsu sun bayyana fa’idar matakin.

A ranar farko ta dage dokar haramta hawa baburan dai, babu babura da yawa da ke yawo a cikin birnin, domin kuwa da dama daga cikin masu babura sun sayar da su sauran kuma sai a yau ne suka fito da su suka kai su wajen gyara lamarin da ya sa masu gyaran babura a jihar kakarsu ta yanke saka.

Za a dai kwashe tsawon wata daya ana aiki da wannan mataki a matsayin gwaji inda daga karshe mahukuntan za su yanke shawarar dage dokar haramta hawan baburan baki daya ko kuma komawa aiki da ita.