1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bazoum: Za mu marabci sojin Turai a Nijar

Mouhamadou Awal Balarabe
February 18, 2022

A wata hira da 'yan jarida, Shugaba Mohamed Bazoum na Nijar ya tabbatar da cewa kasarsa za ta marabci sojojin rundunar Takuba, bayan janyewar dakarun Faransa da na Turai daga Mali.

https://p.dw.com/p/47EYS
Deutschland l Besuch des Nigerianischen Präsidenten in Berlin
Hoto: Presse- und Kommunikationsdienst der Präsidentschaft von Niger

 A wata wata hira da jaridar Le Figaro ta Faransa kwana daya bayan sanarwar janye sojojin Faransa a Mali, Malam Bazoum ya yi imanin cewa ficewar sojojin na Turai za ta haifar da wani gibi a yaki da kungiyoyin 'yan ta'adda idan kasashen yankin Sahel ba su tashi tsaye ba.

A daya hannun kuma, shugaban na Nijar ya yi kakkausar suka ga mahukuntan kasar ta Mali dangane da tsaiko da suka haifar, wanda ya kai Faransa da kasashen Turai  janye sojojinsu daga kasar. Sai dai ya ce burinsa shi ne tabbatar da tsaron kan iyakar Nijar da Mali, saboda haka gwamnatinsa za ta bada damar kafa sabbin sansanonin soji a kusa da iyaka da Mali

Tsaro ya tabarbare matuka gaya a kan iyakar Nijar tun bayan tagawayen juyin mulkin sojoji a Mali, wanda ya haddasa matsin lambar ‘yan ta'adda.