Ziyara Angeller Merkell a gabas ta tsakiya. | Labarai | DW | 04.02.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Ziyara Angeller Merkell a gabas ta tsakiya.

Shugabar gwamnatin Jamus Angeller, wadda a halin yanzu ke riƙe da matsayin shugabar ƙungiyar gamayyar turai ,na ci gaba da rangadi a gabas ta tsakiya , da zumar taimakawa, wajen kawo ƙarshen tashe-tashen hankulla a wannan yanki.

A matakin farko na wannan wannan ziyarce –ziyarce ta gana yammacin jiya, da shugaban ƙasar Masar Osni Mubarack, inda su ka tantanna batun rikici, tsakanin Isra´ila da Palestinu.

A sakamakon wannan ganawa Angeller Merkell ta nunar da cewa:……………………………………………………..

„Mun cimma daidaito a kan cewar: rikicin Isra´ila da Palestinu, rikici ne,da yayi rassa a sasa daban-daban, a game da haka, warware shi, na buƙatar tsoma bakin duk wanda ke da alhakin faɗa aji a wannan yanki“.

Masu kulla da harakokin a yankin gabas ta tsakiya,na nunar da cewa afakaice, Merkell na nufin tsoma bakin Syria da Iran.

Ita ma kasar Russia ta bada shawara saka wannan ƙasashe 2, matakin da Amurika ya zuwa yanzu, ke matuƙar adawa da shi.