1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gaza: Zanga-zangar adawa da harin asibiti

Lateefa Mustapha Ja'afar
October 18, 2023

Harin da aka kai wani asibiti a yankin Zirin Gaza da ya halaka kimanin mutane 200, ya janyo kakkausar suka daga kasashen Larabawa ciki har da kawayen Isra'ila a yankin.

https://p.dw.com/p/4XhHK
Lebanon | Beirut | Zanga-Zanga | Hari | Isra'ila | Asibiti | Zirin Gaza
Zanga-zangar adawa da harin da aka kai asibiti a Zirin Gaza a LebanonHoto: Houssam Shbaro/Anadolu/picture alliance

Tuni dai zanga-zangar yin tir da harin da aka kai asibitin na Zirin Gaza ta barke a kasashen Lebanon da Jordan da Libiya da Yemen da Tunisiya da Turkiyya da Maroko da Iran da kuma yankin Gabar Yamma da Kogin Jordan da Isra'ilan ta mamaye, inda kuma ake shirin gudanar da karin zanga-zangar bayan kiran "ranar nuna takaici" da aka yi a yankin. Koda kasashen Hadaddiyar Daular Larabawa da Bahrain da suka sanya hannu kan yarjejeniyar kawance da Isra'ila a shekarar 2020 karkashin yarjejeniyar Abraham, sun yi tir da harin da aka kai a asibitin na Gaza.