1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Harin bam ya haddasa mace-mace a asibitin Gaza

Mouhamadou Awal Balarabe
October 18, 2023

Yayin da kungiyar Hamas da ke mulkin zirin Gaza ta zargi Isra'ila da laifin kai wannan hari da ya haddasa mutuwar daruruwan mutane, ita kuma Isra'ila ta dora alhakin lamarin a kan 'yan gwagwarmaya na Falasdinu.

https://p.dw.com/p/4XfMq
Mutane da dama sun mutu a harin asibitin zirin Gaza
Mutane da dama sun mutu a harin asibitin zirin GazaHoto: Mohammed Al-Masri/REUTERS

Wani harin roka da aka kai a wani asibiti na zirin Gaza da ya kashe daruruwan mutane na barazana ga yunkurin kasa da kasa na hana yaduwar tashe-tashen hankula a yankin Gabas ta Tsakiya. Yayin da kungiyar Hamas da ke mulkin zirin Gaza ta zargi Isra'ila da laifin wannan hari, ita kuma Isra'ila ta dora alhakin lamarin a kan kungiyar 'yan gwagwarmaya ta Falasdinu ta  Jihadil Islami.

Karin bayani: Kokarin sako Isra'ilawa daga hannun Hamas

Sashen hulda da jama'a da yada labarai na Hamas wacce kasashen Yamma suka dauka a matsayin kungiyar ta'addanci, ya bayyana harin da aka kai a wani asibitin a matsayin "laifi na yaki." Amma firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya yi kakkausar suka tare da musanta hannu kasarsa a wannan lamari.

Karin bayani: Neman mafita a rikicin Isra'ila da Hamas

Sai dai a wani mataki mai kama da mayar da martani, kasar Jordan ta soke wani taron kolin da aka shirya gudanarwa a birnin Amman wanda zai hada da shugaban Amurka Joe Biden da sarkin Jordan Abdullah da shugaban Masar Abdel Fattah al-Sisi da shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas.

Karin bayani: Zirin Gaza: Goyon baya daga Larabawa

Shugabannin kasashe da gwamnatocin kasashen EU na son yin amfani da dukkan hanyoyin diflomasiyya da siyasa don hana yaduwar rikicin yankin gabas ta tsakiya. shugaban Majalisar Tarayyar Turai Charles Michel ne ya bada wannan tabbaci bayan wani taro na musamman da suka gudanar a kan tashin hankalin da ke wakana tsakanin Isra'ila da Hamas.

Karin bayani: Gaza zai iya ruruta rikicin Isra'ila da Hezbollah

Babban jami'in ya ce ta'azzarar rikici zai kasance babban kalubale ga nahiyar Turai musamman a daidai lokacin da yaki ke kara kamari a Ukraine. Sai dai Michel ya jaddada cewa dole ne farar hula da ke bukatar agaji a zirin Gaza su samu ruwa da wutar lantarki da abinci da kuma kula da lafiya. Sannan ya ce an kama hanyar cimma matsaya ta kut-da-kut da Majalisar Dinkin Duniya kan wannan batu.