1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaIsra'ila

Kokarin sako Isra'ilawa a Zirin Gaza

October 12, 2023

Kungiyar agaji ta Red Cross ta ce tana cikin tattaunawa da kungiyar Hamas da kuma hukumomin Isra'ila domin sako mutanen da aka yi garkuwa da su a lokacin barkewar yaki tsakanin bangarorin biyu.

https://p.dw.com/p/4XQo8
Kokarin sako Isra'ilawa daga hannun Hamas Hoto: MOHAMMED ABED/AFP

A cikin sanarwar da kungiyar agajin ta kasa da kasa ta fidda ta ce a shirye ta ke da ta kai wa wadanda aka yi garkuwar da su dauki tare kuma da saukaka sadarwa tsakanin su da iyalansu, sai dai kuma ta bukaci bangarorin da ke yaki da zu saukaka wa fararen hula radadin tashin hankalin wanda kawo yanzu ya tilasta wa sama da mutum dubu 300 tserewa daga Zirin Gaza.

Hukumomin Isra'ila sun ce akalla mutane 150 ne kungiyar ta Hamas ta yi garkuwa da su yayin da darurruwan mutane suka yi batan dabo kana kuma ake ci gaba da tantance gawarwaki.

Karin bayani: Shirin kai kayan agaji Gaza ta Masar

A ranar Laraba (11.10.2023) shugaban kasar Turkiyya Recep Tayib Erdogan ya kaddamar da tattauwa da kungiyar Hamas kan neman sakin mutanen da take tsare da su kamar yadda wata majiya ta kusa da shugaban ta tabbatar wa kanfanin dillanci labaran Faransa na AFP.

Karin bayani: Erdogan ya soki rikicin Gabas ta Tsakiya

A daya gefe kuma ma'aikatar harkokin wajen Brasil ta sanar da cewa kasar da ke jagorantar kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ta kira wani sabon taro na wannan hukuma a ranar Jumma'a (13.10.2023) domin sake duba halin da ake ciki a Isra'ila da Zirin Gaza.

Dama dai Brazil din ta kira wani taro makamancin wannan a ranar takwas ga watan Oktoba sai dai aka gaza cimma matsaya a game da yin Allah wadai da farmakin da kungiyar Hamas ta kaddamar wanda kawo yanzu ya yi ajalin 'yan Isra'ila 1.200 da kuma Falasdinawa 1.200 da suka hada da fararen hula a hare-haren ramuwar gayya da sojojin Isra'ila suka kai Zirin Gaza.

Karin Bayani: Sojojin Isra'ila sun yi wa Gaza kawanya

Shugaban na Brazil Lula da Silva ja jaddada cewa dole ne kungiyar Hamas ta saki yaran da ta kama sannan kuma dole ne Isra'ila ta dakatar da hare-haren da ta ke kai wa Zirin Gaza domin bai wa mata da yara damar ficewa daga yankin i zuwa Masar cikin tsanaki.