Yemen ta na cikin kasashen Larabawa na yankin Gabas ta tsakiya, kuma a shekarar 1990 aka hade yankunan arewaci da kudancin kasar.
Ta kasance kasa mai fama da talauci da yawan rikice-rikice, sannan kasar Saudiyya tana da tasiri a siyasa da rayuwar mutanen kasar.