Zabuka a kasashen Afirka da dama | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 23.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Zabuka a kasashen Afirka da dama

Zabe a Cote d'Ivoire da kuri'ar raba gardama a Kwango Brazzaville da kuma rikicin Boko Haram a Najeriya sun dauki hankalin jaridun Jamus.

Za mu fara sharhunan jaridun na Jamus kan nahiyarmu ta Afirka da jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung wadda ta rubuta sharhi kan zaben shugaban kasa a Cote d'Ivoire a wannan Lahadi.

Ta ce bisa ga dukkan alamu 'yan kasar ta Cote d'Ivoire ba sa nuna wata sha'awa ga zaben. Idan aka yi la'akari da yawan katunan zabe da aka raba a matsayin mizanin auna yawan mutanen da za su kada kuri'a a zaben na wannan Lahadi, za a ga cewa yawansu bai kai kashi 50 cikin 100 ba. Wannan na zama wani hannunka mai sanda ga Shugaban kasa Alassane Ouattara mai shekaru 73, da ke neman sabon wa'adin mulki na shekaru biyar. Bayan tashin hankalin da ya auku a shekarar 2011 biyo bayan zaben shugaban kasa da suka fafata da tsohon shugaba Laurent Gbabgo, Ouattara ya dare kan kujerar mulki. Babbar matsalar shugaban a yanzu ita ce rarrabuwar kawunan tsakanin al'ummomin kasar. Ko shakka babu Ouattara ne zai lashe zaben na wannan Lahadi domin babu wani babban dan adawa da zai kalubalance shi. Saboda haka dole ne shugaban ya yi amfani da wannann dama wajen neman sulhu tsakanin al'ummomin kasar ta Cote d'Ivoire.

Matakin yi wa kundin tsarin mulki karar tsaye a Afirka

Ita kuwa jaridar Süddeutsche Zeitung tsokaci ta yi kan shugaban kasar Kwango Brazzaville:

Afrika - Beginn des Gipfels der Afrikanische Union

Dennis Sassou Nguesso a tsakiyar takwarorinsa shugabannin Afirka

Ta ce Shugaba Denis Sassou-Nguesso ba shi ne shugaban Afirka na farko da ya yi kokarin sauya kundin tsarin mulkin kasa don ya ci-gaba da rike madafun iko ba. A shekarun baya takwarorinsa na kasashe irinsu Gabon da Chadi da Yuganda da kuma Kamaru sun dauki irin wannan mataki don su kafe kan kujerar mulki. A wannan Lahadi ake gudanar da kuri'ar raba gardama kan cire wa'adin shugabanci da kuma yawan shekarun shugaban kasa daga kundin tsarin mulki, da ka iya zama karan tsaye ga aniyar shugaban mai shekarun 71, da ke neman tsayawa takara a zaben shekarar 2016. Sai dai alamu na nuna cewa matasan kasar za su koyi da takwarorinsu na wasu kasashen Afirka wajen taka wa Shugaba Sassou-Nguesso biriki.

Rikicin 'yan tarzoma ya ki ci ya ki cinyewa a Najeriya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya dauki kwararan matakan yaki da Boko Haram amma har yanzu 'yan tarzoma na ci gaba da aikata ta'asa a kasar, har wayau inji jaridar Süddeutsche Zeitung.

Nigeria - Soldaten an der Grenze zu Niger

Sojojin Najeriya na samun nasara kan mayakan Boko Haram

Ta ce yaki da ta'addanci daya ne a jerin alkawuran da Buhari ya yi lokacin yakin neman zabe, inda ya ce kafin karshen shekara za a samu galaba kan kungiyar ta Boko Haram da ta addabi yankin Arewa maso Gabashin Najeriya. Sai dai duk da jerin matakan da shugaban ya dauka wadanda kuma ake ganin tasirinsu, amma 'yan ta'addar da suka yi mubaya'a da kungiyar IS, suna ci-gaba da aika-aika a yankin da ma a wasu yankunan kasashen Nijar da Chadi da Kamaru da ke kan iyaka da Najeriya.

Matsalar yunwa a Sudan ta Kudu mai fama da yakin basasa

Ita kuwa jaridar Die Tageszeitung labari ta buga game da matsalar yunwa a kasar Sudan ta Kudu.

Ta ce kusan shekaru biyu da barkewar yakin basasa a Sudan ta Kudu halin da mutane ke ciki a kasar ya ta'azzara. Yanzu haka kungiyoyin agaji sun yi gargadin cewa a Sudan ta Kudun mutane miliyan 3.9 ke fama da matsananciyar yunwa yayin da dubu 30 ke fuskantar barazanar mutuwa saboda rashin ci-maka.