Yunkurin kawo zaman lafiya a Ukraine | Labarai | DW | 05.02.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yunkurin kawo zaman lafiya a Ukraine

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da shugaban kasar Faransa Francois Holland na yunkurin samar da zaman lafiya a Ukraine, bayan da suka dauki watanni babu cigaba

'Yan siyasan biyu dai za su fara da kai ziyara birnin Kiev a wannan alhamis kafin su karasa Moskow ranar Juma'a, inda ake sa ran za su gana da shugaban kasar Ukraine Petro Poroschenko da Vladimir Putin na Rasha.

Bisa bayanan da wata majiya ta gwamnatin Jamus ta bayar, ziyarar, ta zama tilas ne bisa la'akari da ta'azarar da rikicin kasarta Ukraine ya yi, musamman a 'yan kwanakin da suka gabata, duk da cewa jami'an diplomasiyyan na Jamus da Faransa sun dade suna neman hanyoyin daidaita lamura.

A waje guda kuma, ministan harkokin wajen Amirka John Kerry ya riga ya fara tattaunawa da 'yan aware magoya bayan Rasha na yankin gabashin Ukraine a birnin Kiev, a nan ne ma ake kyautata zaton cewa NATO za ta tura makaman da shugaba Petro Poroschenko ya bukaci a tura a matsayin goyon bayan kasashen yamma ga shawo kan rikicin. A wata jaridar Jamus mai suna "Die Welt" ne Poroschenko ya bukaci karin makamai na zamani da sojoji na musamman matakin da ya ce ya zama tilas sakamakon ta'azarar rikicin da kuma karuwar adadin fararen hulan da ke mutuwa.